✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu yana kokarin satar wayar wutar lantarki

Ko da aka je wajen, an iske gawarsa

Wani matashi mai matsakaitan shekaru ya mutu yana kokarin satar wayar wutar lantarki a jikin wata na’urar taransufoma da ke rukunin gidaje na Lakeview a Mabushi da ke yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa wajen misalin karfe 4:00 na asuba ne wani magidanci ya fahimci cewa babu wuta a gidansa, duk kuwa da cewa akwai a na makwabtansa.

Daga nan ne sai ya umarci mai gadinsa ya duba cikin taransufoma, inda a nan ne ya ga gawar mutumin a cikinta.

Bayan nan ne kuma aka gano cewa ya mutu.

“Daga nan ne na shaida wa ragowar mazauna yankunan abin da yake faruwa, inda su kuma suka shaida wa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), inda su kuma suka tura jami’ansu zuwa wajen.

Mutumin ya ce jami’an kamfanin bayan zuwansu sun tabbatar da cewa matashin ya mutu ne sakamakon jan da wutar ta yi masa, lokacin da yake kokarin satar wayar lantarkin.

“Hakan ta faru ne sakamakon ya riga ya kwanto wayoyi guda biyu daga jikin taransufomar,” inji wani mazaunin yankin.

Aminiya har ila yau ta gano cewa jami’an kamfanin na AEDC sun kira ’yan sanda, wadanda su kuma suka nemo iyalan mutumin ta hanyar lambobin wayar da aka samu a cikin wayar da ke jikinsa, sannan aka kai gawarsa ofishin ’yan sanda da ke Mabushi a Abuja.

Daga bisani kuma ’yan sanda sun damka wa iyalan mamacin gawarsa.