daya daga cikin wadanda suka fafata a tseren gudun fanfalaki da ya gudana a birnin Landan a ranar Lahadi da ta gabata da wani kamfani da ake kira birgin Money London Marathon ya shirya ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi jim kadan bayan ya tsallake layin tsayawa.
Kamar yadda jami’an shirya gasar suka sanar, mutumin ya yanke jiki ya fadi ne jim kadan bayan ya kai layin da ake tsayawa.
Mutumin mai kimanin shekara 42 ya samu matsala ne bayan an yi biris da shi na tsawon lokaci bayan ya fadi inda aka yi tsammanin yana hutawa ne saboda gajiya amma da aka lura da halin da yake ciki sai aka yi kokarin garzaya wa da shi asibiti, amma kafin a isa rai ya yi halinsa.
Wannan shi ne karo na biyu da wani dan gudun fanfalaki ya mutu a yayin da gasar ke gudana tun cikin shekarar 2012.
A shekarar 2012 ma wata mata ‘yar kimanin shekara 30 mai suna Claire Skuires ta mutu jim kadan bayan ta fadi saboda matsalar bugun zuciya kuma kafin a kai ta asibiti a wancan lokaci rai ya yi halinsa.
Kimanin mutum dubu 36 ne suka fafata a gasar tseren ta Landan a ranar Lahadin da ta wuce kuma kimanin motoci 1,200 ne aka samar don bin masu tseren a baya don dauke wadanda suka samu matsala.
dan kasar Kenya Wilson Kipsang ne ya lashe gasar a bangaren maza yayin da Edna Kiplagat ’yar Habasha ta lashe ta bangaren mata.
Ya mutu a lokacin gudun fanfalaki
daya daga cikin wadanda suka fafata a tseren gudun fanfalaki da ya gudana a birnin Landan a ranar Lahadi da ta gabata da wani kamfani…