✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu a filin kwallo saboda bakin ciki

Wani mutum dan kimanin shekara 42 mai suna Ray Dunning ya fadi matacce a lokacin da ya tabbatar kulob dinsa ya samu koma baya (relegation)…

Wani mutum dan kimanin shekara 42 mai suna Ray Dunning ya fadi matacce a lokacin da ya tabbatar kulob dinsa ya samu koma baya (relegation) a gasar rukunin ’yan dagaji (Championship) na kasar Ingila a karshen makon jiya.
Mutumin yana daga cikin magoya baya su kimanin dubu biyu da suka yi tattaki don kallon wasa a tsakanin kulob dinsu Doncaster Robers da kuma na Leicester City da ya gudana a garin Midland.&nbsp Kuma wasan shi ne na karshe a kakar wasa ta bana da zai ba su damar zama ko kuma samun koma baya a gasar.
Rahotanni sun ce Ray Dunning ya kamu da rashin lafiya ne jim kadan bayan an jefa wa kulob din Doncaster kwallo a raga da hakan ta nuna kulob din ya shiga sahun wadanda suka samu koma-baya a kakar wasa mai zuwa&nbsp (relegation). &nbsp
Duk kokarin da wadanda ke tare da shi a lokacin da al’amarin ya faru don ceto ransa&nbsp abin ya ci tura&nbsp inda aka garzaya da shi asibiti amma kafin a isa rai ya yi halinsa.
Tuni mahukunta kulob din suka bayar da sanarwar faruwar hakan a yanar sadarwasu inda suka nuna alhini da kuma yi wa iyalan mamacin jaje.
An tashi wasan ne kulob din Leicester ya doke na Doncaster Robers ci 1-0.