Wani matashi ya yi wa masoyiyarsa dukan kawo wuka har ya aika ta lahira bayan wani sabani ya taso a tsakaninsu.
Ana zargin mutumin ya yi ta jibgar Esther mai shekara 18 ne da tsakar dare har sai da rai ya yi halinsa a layin garejin Ebis Mechanic da ke Yenagoa, babban birnin Bayelsa.
- Noman kashu zai samar da ayyuka 500,000 a Najeriya
- Nakasassu sun tare ofishin gwamna kan kin daukar su aiki
- Yadda masu karbar haraji suka ‘hallaka’ wani direba
Shaidu sun ce rikici ya kaure tsakanin masoyan da suka haifi diya mai shekara biyu ne kan kudin abinci da kuma kula da gida.
Makwabta sun shaida wa Aminiya cewa masoyan sun saba fada da juna, amma a wannan karon kururuwarta na neman ceto ne ya tashe su da tsakar dare misalin karfe 11.30 ranar lahadi.
“Da wasu daga cikinmu suka je sai suka samu an kulle kofar daga cikin dakin.
“Da muka balla kofar sai muka tarar da ita a kwance a tsakar dakin, muka yi kokarin debo ruwa mu yayyafa mata ta farfado saboda a zatonmu suma ta yi, ashe rai ne ya yi halinsa.
“Nan take muka tsare mutumin muka kuma sanar da ’yan sanda”, inji shi.
Ana zargin mutumin ya yi amfani da babban madoki ne ya daki Esther wanda ya yi sanadin mutuwarta, wasu kuma na zargin ta sha tsananin shaka ne, shi yasa ta mutu.
Tuni dai wakilan kungiyar kare hakkin jinsi wadda Matar Gwamnan Bayelsa, Glory Diri suka ziyarci wurin da abun ya faru.
Barista Dise Sheila Ogbise, wanda shi ne mataimakin mai kula da kungiyar, ya bayyana wa ’yan jarida cewa, abun takaici ne, ya kuma yi kira da jama’a da su guji rikicin cikin gida da cin zarafin ’ya’ya mata.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar, SP Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce tuni jami’ansu a caji ofis din da ke Ekeki suka cafke wanda ake zargin don ci gaba da gudanar da bincike.