’Yan sanda a kasar Indiya sun kama wani ma’aikacin agaji da ya fusata bisa zarginsa da banka wa wani banki wuta a Jihar Karnataka bayan an hana shi bashi.
Wanda ake zargin mai suna Wasim Hazaratsab Mulla, mai shekara 33, ma’aikacin ba da agaji daga birnin Haveri, kuma ya je Bankin Canara a jihar don neman rancen Rupee miliyan 1.6 (kimanin Naira miliyan 8 da dubu 966 da 592) a watan Disamban bara.
Daga karshe an ki amincewa da bukatarsa, saboda sabani a cikin takardun da aka mika, wadanda suka saba manufofin bankin.
Wasim dai bai yi nazarin ka’idojin bankin da kyau ba, inda ya hau babur dinsa zuwa reshen bankin a ranar Lahadi, 9 ga Janairun 2022, inda ya bude taga ya fesa wani sindari a ciki tare da banka wa ginin wuta.
Shaidu sun ce sun ga hayaki yana tashi daga ginin kuma nan take suka sanar bayan tashin karar kararrawa alamar gobara tana ci. Mutanen yankin sun tsare fusataccen mutumin har sai da ’yan sanda suka iso.
“Wasim ya fusata ne bayan da aka ki amincewa da bukatarsa ta neman bashi. Ya fesa wasu sinadarai masu konewa inda suka hadu da wuta, watakila man fetur ya sa, amma ana kan bincike kan lamarin,” wani dan sanda ya shaida wa kafar labarai ta National.
“Yana jagorancin wata kungiya mai zaman kanta. Ya nemi kudin sayen injuna, hakan ya sa ya nemi rancen Rupee miliyan 1.6. Abin farin ciki, babu tsabar kudi ko zinariya ko wasu abubuwa masu daraja da aka lalata sanadiyyar kona bankin,” inji shi.
Jami’an kashe gobara sun yi nasarar kashe gobarar, amma ’yan sanda sun ce, kwamfutoci biyar da fankoki da na’urori iri-iri da fitilun da darajarsu ta kai ta Rupees miliyan 1.2, (kimanin Naira miliyan 6 da dubu 641 da 920) sun kone.
Ana tuhumar Wasim Hazaratsab Mulla da laifin kona bankin kuma yana jiran a yanke masa hukunci.