✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe surukinsa kan fada da mahaifiyarsa

Ya kashe surukinsa saboda surukin nasa ya mari mahaifiyarsa.

Wani matashi ya aika surukinsa lahira saboda surukin nasa ya mari mahaifiyarsa.

Dattijon ya mari tsohuwar mai shekara 75 ne bayan wata takaddama ta kaure a tsakaninsu, amma makwabta suka shiga tsakani.

Aminiya ta gano cewa bayan dawowar matashi da dare ne aka labarta masa abin da ya faru, shi kuma ya tunkari tsohon, a nan ne hatsaniya ta kara barkewa.

Ana cikin yamutsin ne matashin ya sari surukinsa da adda a kai a da sauran sassan jikinsa, aka dauke shi zuwa asibiti, amma ya ce ga garinku nan.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta tabbatar da faruwar lamarin a kauyen Ate daura da Igarra, a Karamar Hukumar Akoko Edo.

Kakakin Rundunar, SP Kontons Bello, ya ce matashin na hannu, ya kuma amsa laifin.

Amma ya ce ya yi hakan ne don kare kansa, saboda surukin nasa ne ya fara dauko makami zai sare shi, shi kuma yare kansa.

Jami’in ya ce nan gaba za a kammala bincike kan lamarin da ya faru ranar Juma’a domin gurfanar da wanda ake tuhumar a gaban kotu.