✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe makwabcinsa kan wurin ajiye mota

Wani mutum ya caka wa makwacinsa wuka ya kashe shi saboda sababin da suka samu a kan wurin ajiye mota.

Wani mutum ya caka wa makwacinsa wuka ya kashe shi saboda sababin da suka samu a kan wurin ajiye mota.

Lamarin ya faru ne a yankin AJah na Jihar Legas, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar.

Ya ce rundunarsu ta tsare wani mutum mai shekara 41 da ya caka wa makwabcinsa wuka a ciki, ya kashe shi nan take, bayan sun samu sabani kan wurin ajiye mota a kan layin Gbadamosi  da ke Rukunin Gidaje na Badore a daren Asabar.

Hundeyin ya ce an kai rahoton abin da ya faru ofishin ’yan sanda na Langbasa kafin wayewar garin Lahadi.

“’Yan sanda sun je sun dauki hoton abin da ya faru, kuma an kai gawar mutuwarin IDH da ke Yaba domin gudanar da bincike,” wanda ake zargin kuma ana tsare da shi.