✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe dan uwansa a fadan kungiyar asiri

Za a mika shi kotu tare da sauran wadanda aka kama su tare don zurfafa bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta cafke wani matashi kan zargi da kashe dan uwansa da nufin yin asiri.

An kama shi ne a cikin wasu ’yan kungiyar asiri 54 da aka kamo bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Edo na a cafko wasu ’yan kungiyar asiri da ake nema.

“A unguwarmu, muna sayar da tabar wiwi don mu samu kudi,” inji matashin dan asalin yankin Sabogida-Ora da ke karamar hukumar Owan ta Yamma a Jihar.

Sai dai ya ce a lokacin da rikici ya barke a tsakanin ’yan kungiyar asirin biyu, baya wajen balle ya samu masaniyar abin da ya faru.

“Bana wajen lokacin da suka kashe dan uwana, ban san lokacin da suka kawo farmakin ba.

Sai dai kwamishinan ’yan sandan jihar, Philip Aliyu Ogbadu, y ace za a mika wanda ake zargin tare da wasu zuwa kotu don ci gaba da bincike a kansu.

%d bloggers like this: