✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe budurwarsa, ya binne gawar a dakinsa

An kama wani matashi bayan ya makure budurwarsa har sai da ta mutu, sannan ya binne gawarta a cikin dakinsa.

An kama wani matashi bayan ya makure budurwarsa har sai da ta mutu, sannan ya binne gawarta a cikin dakinsa.

Matashin da ake zargi yana yin tsafin samun kudi ne, ya yi wa budurwar tasa aika-aikan ne ranar Alhamis, a unguwar Okaka da ke garin Yenagoa, hedikwatar Jihar Bayelsa.

Bayan dubunsa ta cika, wani makwabcinsu ya ce mutanen unguwar na zargin shi da zama dan Yahoo-Yahoo ya saba kawo ’yan mata daban-danan dakinsa.

Daga bisani jami’an tsaro su cafke matashin, lamarin da ya sa mazauna unguwar cikin al’ajabi.

Kakakin ’yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce: “Matashin mai shekara 27 dan asalin unguwar Ikibiri ne, amma yana zaune a unguwar Okaka,

“Ya binne gawar budurwarsa, Kate Ogwoh, mai shekara 26, Kate Ogwoh, bayan ya makure ta har ta mutu.

“An tsare shi ne bayan bayanan sirri daga makwabta a ranar 29 ga watan Yuli da misalin karfe 8 na safe.

“Yanzu haka yana fuskantar bincike a Sashen Binciken Manyan Laifuka.”