✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe abokinsa saboda ya nemi yin luwadi da shi

Wani matashi da ake zargi da kashe abokinsa da suka hadu ta kafar sada zumunta ta Facebook ya shaida cewa, ya kashe abokinsa ne saboda…

Wani matashi da ake zargi da kashe abokinsa da suka hadu ta kafar sada zumunta ta Facebook ya shaida cewa, ya kashe abokinsa ne saboda ya matsa lallai sai ya yi luwadi da shi.

Wanda ake zargin mai shekaru 28 mai suna Angus Chukwebuka Nwankwo da kaninsa Chidiebere Omeyi suna cikin mutum sama da 100 da rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta gabatarwa ‘yan jaridu a hedikwatar rundunar da ke Amawbia a karamar hukumar Awka South South.

Ya ce, ya hadu da abokin nasa ne ta kafar Facebook wanda ya yi masa alkawari zai ba shi Naira dubu 20 idan ya yi luwadi da shi, ya ce da farko ya ki ya amince, amma daga bisani ya amince masa inda suka yi zasu hadu da shi a yankin Nanka.

“Daga nan sai ya taso daga jihar Imo ya iske ni tare da kanina da yazo sai nace ya bani kudin Naira dubu 20, sai ya ce sai ya biya bukatarsa kafin ya bani, sai fada ya kaure a tsakaninmu, ya bugamin itace, daga nan kanina ya rike shi na kwace itacen na buga masa har ya mutu.” In ji shi.

Ya ce, shi da kaninsa sun kai kansu ga kungiyar ‘yan sa kai na kato da gora saboda babu ofishin ‘yan sanda a yankin.

Haka zalika, dan uwan wanda ake zargin ya shaidawa manema labarai cewa, yayansa ya sanar masa wani dan luwadi zai zo wajensa daga jihar Imo da zummar yin luwadi da shi, amma shi ba zai yadda ba, zai karbi kudinsa ne kawai ya kyale shi, “Dan uwan nawa ba dan luwadi bane, yana yin aikin wasan kwaikwayo ne da waka sannan yana koyan aikin famfo a Legas, yazo gida bikin jana’iza ne.” In ji shi.