✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe abokinsa saboda musu kan wa ya fi a tsakanin Messi da Ronaldo

Wani abin al’ajabi ya faru a Indiya a karshen makon jiya bayan wadansu ’yan Najeriya biyu da ke zaune a Indiya suka kaure da musun…

Wani abin al’ajabi ya faru a Indiya a karshen makon jiya bayan wadansu ’yan Najeriya biyu da ke zaune a Indiya suka kaure da musun kwallo a kan wa ya fi a tsakanin shahararren dan kwallon Ajantina Lionel Messi da kuma shahararren dan kwallon Fotugal Cristiano Ronaldo.
Jaridar The Mirror wacce ta kalato labarin a yanar gizo ta nuna yadda musu a tsakanin wa ya fi iya kwallo a tsakanin Messi ko Ronaldo ya kaure a tsakanin magoya bayan biyu.  Shi mai goya wa Messi baya mai suna Obinna ne ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa (birthday party) a gidansa inda al’amarin ya faru.  Al’amarin ya faru ne a yankin Nalasopara da ke birnin Mumbai na Indiya.  Rahoton ya nuna dukkan ’yan Najeriyar suna zaune ne a Indiya.
Kamar yadda wani jami’in hukumar ’yan sanda na yankin mai suna Kiran Kabadi ya shaida wa manema labarai, ya ce wani dan Najeriya mai suna Obinna da ya ke bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekara 34 shi ya fara jifan wani abokinsa mai goya wa Ronaldo baya mai suna Nwabu da kofin gilas amma bai same shi ba saboda kawai suna musu a tsakanin wa ya fi iya kwallo a tsakanin Messi da Ronaldo.  Hakan ta sa shi kuma Nwabu ya yi wuf ya dauki wani bangaren kofin gilashin da ya tarwatse ya nufi Obinna inda ya rika caka masa a sassan jikinsa har sai da ya ga ya zube a kasa ba ya numfashi.  Nan fa jama’ar da ke wurin kowa ya ranta cikin na-kare inda jami’ansa suka yi nasarar cafke Nwabu wanda ya aikata laifin Nwabu don gudanar da bincike.
Jami’in ’yan sandan ya nuna da zarar sun kammala bincike za su tura mai laifin zuwa kotu don a yi masa hukuncin da ya dace.
Al’amarin sarkewar gardama a kan wa ya fi iya kwallo a tsakanin Messi da Ronaldo ba sabon abu ba ne a sassan duniya. Ko a Najeriya hakan ta sha faruwa sai dai ba a taba samun labarin yin kisa a kan haka ba.