Wani abin al’ajabi ya faru a Unguwar Juma da ke cibin birnin Zariya da ke Jihar Kaduna inda wani matashi mai suna Sama’ila ya yi kwance-kwance ya caka wa abokinsa mai suna Yakubu Umar da aka fi sani da Abba dan kimanin shekara 18 almakashi a wuya saboda musun kwallo da hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Malam Abubakar Abba wanda yake rike da marigayin mai suna (Abba) don dan wansa ne, ya shaidawa Aminiya yadda alma’amarin ya faru kamar haka: “ Ina da yaron wana wanda aka mutu aka bar mini don cigaba da rike shi mai suna Yakubu Umar (Abba) mai shekaru 18 da haihuwa inda wasu suka shaida mini cewa ga shi can kwance cikin jini. Na yi gaggawar zuwa wurin inda na same shi cikin wannan hali daga nan na garzaya da shi asibiti amma da isarmu sai rai ya yi halinsa.
Da na tantudi wadanda abin ya faru a gabansu wato abokansa sai suka ce abokinsa ne Ismaila Musa ya caka masa almakashi a wuya a lokacin da suke gardama irin ta kwallon kafa. Suka ce da ma tun da jimawa Isma’ila yana cewa sai ya kashe (Abba) don haka a wannan rana da wannan abu zai fara sai da suka ci abinci tare bayan sun kammala ne wannan takaddama ta kwallo ta sarke a tsakaminsu wanda ya kawo kisa a ciki”
Malam Abubakar ya cigaba da bayanin cewa da yake (Abba) ya rasu ban yi kasa a gwiwa ba na shaidawa jami’an tsaro da kuma uwar kungiwar mu ta Izala da ke Zariya don suna da hannu a kan yadda suke tallafawa rayuwar Abba saboda ba ni da karfin arzikin daukar dukkan dawainiyarsa, daga nan muka yi masa sallah irin na addinin Musulinci muka rufe shi.
Ya ce jami’an tsaro sun kama Sama’ila inda yanzu haka suna tsare da shi don cigaba da gudanar da bincike sai dai maganar biyan diyya sai abin da ya biyo baya kasancewar ana tattaunawa a tsakanin iyayen yaron da ya yi kisan kai da kuma mu da aka kashewa da.
A hirar da wakilinmu ya yi da yaron da ya yi kisan kan watau Sama’ila, ya yi nadama ne a kan abin da ya aikata na kashe abokinsa kuma ya ce bai aikata wannan aiki a cikin maye ba, don ba ya shan kwaya ko giya sai dai tsautsayi ne ya kawo haka.
Aminiya ta tuntubi hukumar ’yan sanda da ke cikin birnin Zariya inda babban jami’in tsaron ya tabbatar masa da aukuwar wannan lamari. Ya ce nan ba da jimawa ba ne za su aika da yaron da ya yi kisan kan zuwa Kaduna don a cigaba da gudanar da bincike.
Ya kashe abokinsa a kan musun kwallo
Wani abin al’ajabi ya faru a Unguwar Juma da ke cibin birnin Zariya da ke Jihar Kaduna inda wani matashi mai suna Sama’ila ya yi…