Daya daga cikin Dattawan Arewa a Kurmi, Sardaunan Ore Alhaji Sani Kangiwa ya ce yana goyon bayan masu bayar da shawarar a dakatar da fataucin kayan abinci daga Arewa zuwa sashin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu na tsawon wata uku domin hakan ya zama darasi ga mutanen yankin su gane kuskuren da suke tafkawa na auka wa Hausawa ko ’yan Arewa da ke zaune a yankunansu.
Sardunan na Ore ya kuma bukaci Gwamnonin Arewa da sarakunansu ne za su iya yin maganin takurawar da ake yi wa jama’arsu da ke zaune a yankunan Kudu.
- An gurfanar da likita ya yi wa matar aure fyade a asibitinsa
- Gwamnati za ta yi wa ’yan gudun hijira katin shaida —Pantami
- Hadimin Ganduje ya gwangwaje matasa da tallafin Jakuna
- An sace jariri bayan kwana uku da haihuwa
“Idan gwamnoni da sarakuna da dukkan masu fada-a-ji daga Arewa suka hanzarta daukar matakin mika shawara da bukatunsu ga takwarorinsu na Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, to za a iya maganin matsalar kabilanci da al’ummar wannan sashe na Kudu suke nunawa ga ’yan Arewa, inda ake hana su sayen gidaje da hana su gina wuraren ibada da makarantun koyar da ’ya’yansu ilimin addini”, inji shi.
Ya ce, “shirun da shugabannin Arewa suka yi a kan wannan babbar matsala da ta shafi zamantakewar al’ummar Najeriya ce ya taimaka wajen karuwar lamarin”.
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya kawo shawarar cewa kamata ya yi shugabannin Arewa su yi aiki da hikima da basirar da Allah Ya ba su wajen nuna wa duniya irin yadda al’ummomin Kudu suke mike kafa wajen gudanar da harkokinsu lami lafiya a Arewa, ba tare da takura musu ba
Ya ce “Hatta tattalin arzikin Arewa kusan kashi 60 cikin 100 yana hannun ’yan Kudu ne, inda suke zaune a gidajensu da gina wuraren ibadarsu da gina makarantun koyar da ’ya’yansu da samar da guraben aiki ga mutanensu a Arewa, ba tare da tsangwama ba amma abin bakin ciki, ba haka lamarin yake a Kudu ba; inda ake hana ’yan Arewa cin irin wannan moriyar rayuwa”.
Ya ce “Ba zan taba mantawa ba a zamanin mulkin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, ya amince da sanya shugabannin kabilun Kudu cikin hakimansa da ake biyansu albashi a kowane wata a Masarautar Kano.
“Duk an yi haka ne domin kyautata zamantakewa da zama lafiya. Amma a sashin Kudu baki daya babu inda wani Sarkin Hausawa ko Sarkin Fulani ya samu irin wannan moriyar”.
Ya ce, “Sai shugabannin Arewa da kafafen labaransu sun yi da gaske wajen nuna wa duniya musamman al’ummomin Kudu su fahimci irin garabasar da mutanensu da shugabanninsu suke samu a Arewa ne hakan zai taimaka wajen kawo karshen irin wannan kazamin kabilanci da ake nuna wa ’yan Arewa mazauna Kudu”.
Ya kawo misali da yadda al’ummar Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu suka rika kai wa ’yan Arewa hari da kisan gillar da aka yi musu da kona kadarorinsu a lokacin zanga-zangar #EndSARS kwanan baya.
Sardaunan na Ore ya bayar da shawarar cewa ya kamata shugabannin Arewa su mika irin wannan matsaloli ga Gwamnatin Tarayya domin daukar matakin hana aukuwar irin haka a nan gaba.
Haka kuma ya yi tir da wadansu ’yan Arewa marasa kishi da ake hada kai da su wajen koma-bayan sashinsu.