Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya saurari buƙatun matasan da ke zanga-zangar tsadar a fadin kasar.
Atiku ya yi wannan kira ne yayin da yake jinjina wa ‘yan Nijeriya da suka fito kan tituna domin nuna adawa da matsin rayuwa da ake fuskanta a gwamnatin babban abokin hamayyarsa a zaɓen da ya gabata.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Atiku ya yabawa ‘yan Najeriya bisa jajircewar da suka nuna yayin da ya yi Allah wadai da ɓata garin da suka fake da zanga-zanga suna ɓarna a wasu jihohi.
Ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su lura da yadda suke gudanar da ayyukansu kuma su daina muzguna wa ‘yan jarida da yin harbe-harbe ba gaira ba dalili.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sassauta ya saurari masu zanga-zangar.
“Farkon zanga-zangar da jama’a suka yi a faɗin ƙasar a jiya abin lura ne.
“Wannan zanga-zangar ta buɗe wata hanya mai mahimmanci ga jama’a don nuna rashin amincewa da manufofin gwamnati, tare da fafutikar neman samar da shugabanci nagari a cikin al’ummarmu.
“Yawancin masu zanga-zangar sun gudanar da ita cikin lumana da kwanciyar hankali kuma dole ne a yaba musu saboda kamun kai da ƙwazo.
“Sai dai muna bakin ciki kan yadda a wasu wuraren ake samun rahotannin tashe-tashen hankula, lamarin da ya kai ga yin arangama tsakanin ‘yan sanda da wasu matasa.”