✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ya kamata Sarkin Musulmi ya hana yin kayan aure’

Malamin Musulunci ya bukaci Sarkin Musulmi ya sa baki a soke kayan na gani ina so da na gara

Malamin Musulunci a jihar Sakkwato, Murtala Bello Assada ya bukaci Sarkin Musulmi Muhamma Sa’ad Abubakar ya sa baki a hana yin kayan aure a jihar.

A kiran da ya yi a masallacin da yake karatu a unguwar Mabera, malamin ya ce kayan na gani ina so da na gara na wahalar da masu yin su har ta kai ga sai sun ci bashi suke iya yi.

“Matashi a yanzu ya fi son ya sayi mashin in ya samu kudi domin sayen babur roba-roba ya fi sauki da yin kayan na gani ina so.

“Uba sai ya ranci kudi kafin ya iya kai wa surukinsa shinkafar gara.

“Wwannan matsalar matukar Sarkin Musulmi bai ba da umarnin kashe kayan aure ba za ta kara haddasa fitina bayan wadda ake ciki”, a cewarsa.

Zanga-zangar da matasa a jihar suka gundara a makon jiya neman a soke yin kayan na gani ina so a jihar, ya sa mutane ke ganin lamarin ya munana.

Matasan na neman mahukunta su hana yin kaya a duk lokacin da saurayi ya kai matsaya da budurwar da yake so ya aura; Sadaki kawai za a biya idan magabata sun amince a aura masa ita.

Sai dai wasu na ganin abin da matasan ke nema alama ce da ke nuna sun zama ragaye a tafiyar da lamurransu har suke neman son komai a bagas.

A ganinsu raggonci ne ga namiji ya nemi a dauke masa kyautata wa masoyiyarsa; sakarci ne kuma mutum ya yi abin da yafi karfinsa  don burge mutane.

Don haka suke ganin bai dace ba don wasu sun wuce kima wurin burge mata da duniya masu son banza kuma su ce a fasa kowa ya rasa.