Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci hukumomin Najeriya da su binciki zargin da ake yi wa sojojin kasar na tirsasa wa mata zubar da ciki a sansanonin ’yan gudun hijira.
Mai magana da yawun Babban Sakataren, Stephane Dujarric, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
- Ya kashe wan mahaifinsa ya kone gawar saboda zarginsa da maita
- Gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijirar Najeriya a Nijar
A ranar Larabar da ta gabata ce dai kamfanin dillancin labarai na Birtaniya, Rueters, ya ce ya gudanar da wani binciken sirri, inda a ciki ya zargi sojojin na Najeriya da zubar da cikin mata ba bisa ka’ida ba a yankin Arewa maso Gabas tun shekarar 2013.
A cikin rahoton dai, Reuters ya yi zargin cewa an zubar da cikin manyan mata da ’yan mata kusan 10,000, wadanda akasarinsu wadanda ’yan ta’addan Boko Haram suka sace ne kuma suka yi musu fyade, kamar yadda gwamman shaidun da Reuters ya ce ya tattara tsawon lokacin suka tabbatar.
Stephane Dujarric, cikin wani sakon imel da ya aike wa Reuters ya ce, “Babban Sakataren ya damu matuka da zarge-zargen tilasta zubar da ciki da ake yi wa sojojin Najeriya kan matan da ’yan mata wadanda dama Boko Haram suka riga suka ci zarafinsu.
“Ya kamata a gudanar da zuzzurfan bincike don a yi adalci da hukunta duk masu hannu a ciki.”
Sai dai a ranar Alhamis, Babban Hafsan Tsaro Najeriya, Manjo Janar Lucky Irabor, ya ce ko daya ba za su binciki rahoton ba, saboda sam babu kamshin gaskiya a cikinsa.
Har yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta fito fili ta yi martani ga rahoton ba.
Kazalika, kamfanin na Reuters ya ce duk yunkurin da ya yi na jin ta bakin Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed a kan shawarar Guterres din ta ci tura.