✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Gwamnoni su kiyaye martabar masarautunmu – Sarkin Ningi

Mai Martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya (OON), daya ne daga cikin tsofaffin Sarakuna a Arewacin Najeriya, Sarkin Ningi Ya haura  shekaru 40 yana…

Mai Martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya (OON), daya ne daga cikin tsofaffin Sarakuna a Arewacin Najeriya, Sarkin Ningi Ya haura  shekaru 40 yana sarauta. A yau cikin manyan Sarakunan Arewa Su uku suka fi dadewa kan karagar Mulki, Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris  da Sarkin Jama’are Alhaji Ahmadu Muhammadu Wabi na III. Sarkin ya amsa tambayoyin manema labarai kan rarraba masarautu da gwamnoni keyi musamman rarraba masarautar Kano da gwamnan jihar, Alhaji Abdullahi Ganduje ya yi. Ga kadan daga cikin yadda hirar ta kasance:

 

A matsayinka na daya daga cikin manya kuma tsofaffin sarakuna a Arewacin Najeriya ko yaya sarki ya ga abin da ke faruwa a Jihar Kano na yunkurin rarraba masarautu?

Da fari dai abubuwan da suka faru a Kano ba mu ji dadinsu ba. Na zabi na amsa maka tambayarka ne domin a matsayina a daidai wannan lokacin a duk Arewa ban da Sarkin Zazzau da Sarkin Jama’are, babu wani Sarkin da ya fini dadewa a Sarauta, shi Sarkin Jama’are (Allah ya bashi lafiya) don yanzu haka yana kwance ba lafiya). Ban da wadannan Sarakuna biyun bani da sa’a a sarauta, yawancin kusan dukkanin manya-manyan Sarakunan nan na yanzu na haife su. Na yi zamani da magabatansu da yawa, wasu da kakanninsu ma, wasu kuma nayi Zamani da iyayensu.

Wannan tambayar taka akwai muhimmanci a cikinta a daidai wannan lokacin da muke ciki. na zata dai ‘yan siyasa ko gwamnatoci ina fatan za su iya hakuri da mu a rika mana hakuri, idan mun yi wani abu a mana hukunci wanda ya kamata, ba mai tsanani irin wannan ba.

Ni a ra’ayina abun da ya faru a Kano ba abu ne mai dadi ba; kuma sai dai a baiwa gwamnati hakuri, mai Martaba Sarkin Kano shikuma a bashi shawar-wari. Al’amura irin wadannan, mu yadda muka sani tun lokacin Turawa har su Sardauna ba a cika kai tsaye a karya Sarauta irin wannan ba.

Ita Sarauta tana tafiya ne tare da tarihi da al’adun mutane daga inda aka lala-tata shi kenan tarihin al’umma ya wargaje, idan kuma mutane basu da tarihi ko suka yi watsi da tarihinsu da al’adunsu to su bai kamata a kirasu mutane ba.

Abun da ya faru yanzu gani na ke a baiwa gwamnatin jihar Kano hakuri da majalisar dokokin jihar Kano da Mai Martaba Sarkin Kano ya kamata ne a hadu tare a hada kai ayi aiki wa al’umma tare, a gudu tare a tsira tare. Saboda haka  Abin da ya dace a yi a nan shine a sassauta wannan dokar da majalisa tayi na rarraba masarautar kano, a kuma bi abun a hankali domin girman Sarautar Kano ya shafemu gaba dayanmu Sarakunan Arewa, don haka in ba’ayi hakan ba to fa hakan ba kano kawai zai shafa ba zai shafemune dukkan mu Sarakunan Arewacin Kasar nan.

Idan ka duba a Tarihi Kano tsohowar Masarauta ce data shafe fiye da shekara dubu 2 ko zuwa dubu 3 suke da sarauta tun lokaci Habe har Fulani suka zo, a nan Kasar Arewa babu sarauta irin tasu, sai dai Sokoto, Borno, da Gwandu iyayen gidanmu ne a daraja, amma sarauta tsurarta sai Kano.

Idan aka wulakanta Sarautar Kano to kowa sai ya shafa wa kansa ruwa, a saboda haka ne nake tsokaci a nan nake cewa ita gwamnatin jihar Kano ta yi hakuri, jama’ar jihar Kano su yi hakuri, Mai Martaba Sarki ya yi hakuri, a hadu tare a kyautata jihar Kano da masarautar Kano, amma kar a lalata tarihin al’ummar kano , kar kuma a lalata tarihin sarauta a Arewacin Najeriya.

Ko Sarki zai mana fashin baki kan illar irin wannan hukunci da shi Gwamna ya yi?

In an lura da wannan hukuncin ‘ya’yan sarautar Kano, jama’ar mutanen Kano baki daya, da mu Sarakunan Arewa ko sarakunan Najeriya gaba daya wannan hukuncin zai mana illa. Kamata ya yi a takaita wannan hukuncin ga inda ya auku. Amma yadda aka wargaza wannan al’amarin muna fatan a dai yi tunani akai zuciya nesa. Kano dole idan an yi tafiya irin wannan to dole ne wasu al’amura su  ruguje, wadansu su ja da baya, to kuwa ba abu ne wanda zai yi wa kowa dadi ba, kama daga mutanen Kano, mu sarakunan arewa da ma na Najeriya da kuma ‘ya’yan sarautar Kano duk al’amuranmu zasu ja da baya.

Idan an ce an yi laifi ba mu ki ba, don dai wata kila mai yiwuwa Mai Martaba Sarki ya yi wani laifi  wanda shi mai martaba dan Adam ne shi ba zai gaza kuskure ba, amma irin mataki da hukuncin da gwamna ya dauka ya so ya yi tsanani, hukuncin ya so ya zarce kan Mai Martaba ya so ya shafi dukkanin Kano tun daga Dabo, ya so ya shafi dukkan dan adam din da ke Kano ya so ya shafi dukkanin Sarkin da ke arewa ko Najeriya baki daya . Don haka ina kara cewa a yi nazari sosai kan wannan hukuncin, komai abun da ya faru hakuri shi ne maganin komai.

Akasari siyasa na sa sarakuna shiga cikin wani irin yanayi ko me sarki zai ce a kai?

Abin da nake son a lura shi ne mu Sarakuna muna da dajararmu, yanzu kamar ni din nan ka duba Jihar Bauchi dukkanin gwamnonin da aka yi a kan idona aka yi su, kusan guda 20 hudu a ciki sun rasu sauran suna nan. Don haka mun ga abubuwa da yawa. Kuma wasu lokutan mu sarakuna muna cikin tsaka-mai-wuya  a lokacin siyasa, yawancin ‘yan siyasan nan matsayin da suke dauka shine in ka goyi bayan gwamnati mai ci to baka yi laifi ba; amma in ka goyi bayan ‘yan adawa to ka yi laifi.

To wadannan abubuwan mu kuma dole ne biyayyarmu ta zama wa gwamnati, a kullum za mu yi wa gwamnati biyayya don in jama’armu suka ga muna biyayya su ma za su kara yi wa gwamnati biyayya. Kan sha’anin biyayyar nan ni ina biyayya wa kowace gwamnatin da ta zo amma kuma bana son a shiga hurumina. Idan aka nemi shiga hurumina bana hakuri a nan.

Da can yaya ake hukunta sarki in ya yi laifi?

A takaice dai, irin yadda ake ta fada can baya zuwan Turawa da suka mulke mu shekara 60 da su Sardauna da Tafawa Balewa su ka karbi mulki har aka zo zuwa wannan zamanin, akasari ba a muzanta Sarakai haka, kullum idan Sarki ya yi laifi akwai matakan da ake bi wajen shawo kan matsalar, akan kafa kwamiti a tuntubi sarki hujjojinsa a bi bahasi kafin a yanke hukunci. idan ma za a yi wa Sarki ritaya ko tube masa rawani, ba a cewa an tube Sarki a zamanin Turawa ma da su Sardauna kenan sai a ce Sarki ya yi murabus, duk wadannan abubuwan ana yi ne fa don kare martabar Sarautu.

Yanzu idan gwamnatoci suka ci gaba da tafiya kan wannan matsayar tasu me zai faru gaba?

Idan mun ce yau za mu yi watsi da yadda ake mutunta sarakuna da masarautu a baya ina ganin ba mu kyauta wa kanmu da ya’yanmu ba sannan ba mu kyauta wa jikokinmu ba da sauran mutane masu zuwa nan gaba ba. Kuma al’amuran nan da suke na al’adunmu na gargajiya kamata ya yi a mutunta su, da son samu ne ma a yi wata majalisa wanda Sarkin Musulmi da Shehun Borno da Sarkin Gwandu za su shugabanci majalisar idan wani sarki ya yi laifi, idan gwamnati tana son ta yi hukunci ta ce ga abun da take da shi ga wadannan sarakuna ta wannan majalisar don a ga mene ne ya kamata a yi a kuma bada shawara.

Idan aka ce sarki ya ba da shawara me kake so a yi kan masarautar Kano?

Kamar yadda na fada tun da fari, ina so Ko wani bangare ya yi hakuri a kai zuciya nesa da bangaren Gwamna da bangaren majalisa da bangaren mai Martaba Sarkin Kano. Ina rokon duk abin da za a yi nan gaba ba ma a kano ba ko’ina ne muddin ya shafi Sarki a yi kokari a mutunta kujerar Sarautar, kada a tsaya duba mutumin da ke kan kujerar a duba martabar kujerar, da mutuncinta da tarihinta wajen yin komai.

Babu wanda zai ji dadin irin wannan abun. Ina sake nanatawa a dai yi hakuri, a Kano hakurin ya fi, walau laifi na Sarkin kano ne, ko na gwamnan Kano a tattara a watsar a duba maganar da na yi din nan na cewar wannan hukuncin ba na Sunusi Lamido Sunusi ba ne kawai, wannan hukuncin ya shafi jinsi da yawa, ya shafi ‘yan sararutar kano, sarakunan Nijeriya da sauran wadanda abun ya shafa. Don haka muna rokon a sassauto da wannan dokar ba don kowa ba sai don martabar Kano da sarautar Kano.

Daga karshe fatana shine a samu zaman lafiya a kowani lokaci, a kuma kawo karshen wannan batun raba masarautar Kano domin yin hakan ya shafe mu gaba daya, a kuma danne zuciya a kai zuciya nesa.

Idan aka yi hakan za a samu ci gaba mai dorewa. Allah ya kare mana kasa ya ci gaba da bamu zaman lafiya da wanzuwar zaman lafiya, ya kuma kade dukkanin sharri.