✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Buhari ya yi amfani da shawarar Obasanjo ko ya yi watsi da ita?

Bai kamata Buhari ya dauki shawarar ba – Fatima Adamu Abubakar Rabilu, Gombe Fatima Adamu: “A gaskiya ni ra’ayi na shi ne bai kamata shugaba…

Bai kamata Buhari ya dauki shawarar ba – Fatima Adamu

Abubakar Rabilu, Gombe

Fatima Adamu: “A gaskiya ni ra’ayi na shi ne bai kamata shugaba Muhammadu Buhari, ya dauki shawarar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ba shi ba. Shawarar cewa kada ya fito takara a 2019 ba daidai ba ne domin mu talakawa muna muradin ya kara mulkanmu saboda shugaban talakawa ne. Kuma shi Obasanjo din a lokacinsa ba har karo na uku ya so ya ci gaba da mulki ba? duk da mu ‘yan Najeriya ba kaunarsa muke, ba ballantana Muhammadu Buhari da duk talakan Najeriya ke kaunarsa.”

Buhari ya yi watsi da shawarar Obasanjo kawai – Ado Isah Jume

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Ado Isah Jume: “Bai kamata Obasanjo ya kawo wannan maganar ba saboda mutane ba za su ga aikin wannan gwamnati sai in Buhari ya zarce. Abin da ya sa na fadi haka kuwa shi ne ganin yadda shugaba Buhari ya gama nakaltar dukanin matsalolin kasar nan tare da gano bakin zaren warwarewa. Ina ganin wadanda ba sa so a ga nasararsa ce kawai ba za su so ya ci gaba ba.

Tsarin asusun bai daya da kashe kaifin hare-haren ‘yan boko haram kadan ne daga cikin nasarorin da Buhari ya samu. Sannan irin kudaden shigar da kasar nan ta samu da bunkasar da asusun ajiya na kasar waje ya yi, idan har ba mu ba Buhari dama a karo na biyu ba to tamkar jaki ne da shan bugu gardi da amshe kudi domin ya gama yi wa duk wanda zai dare kan mulki wahala ne ta yadda a karshe ba za a ga kokarinsa ba sai na wanda ya gaje shi. Ina ganin bai kamata Obasanjo ya shigo da wannan batun ba tunda ya yi kira a mara masa baya tun farko.

Bai kamata ya bi shawarar Obasanjo ba – Ibrahim Garba

Umar Mohammad Gombe, Abuja

Alhaji Ibrahim Garba Zariya: “Ko kadan bai kamata Shugaba Buhari ya bi shawarar Obasanjo ba. Wai ma shi Obasajo ya dauka ‘yan Najeriya sun mance ne cewa shi har wa’di na uku ya nema? Amma Allah bai yarda ba, inda hatta mataimakinsa ya hana shi sakat. Kuma batun lafiya a yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi shi lafiya, maganar makiyaya a lokacin da yasa aka kashe mutanen Zaki Biyem tsakanin Jukun fa Fulani meyasa ba’a tsigeshiba kohanashi cigaba da mulkiba? Tattalin arzikin kasa kuma da yace shugaba Buhari bays da ilimi a kai shima lokacin yayi nasa mulkin inginiya ne na gyaran gada inace sai kwanannan ya gama digiri na biyu ba (Master’s?)a Open Unibersity ba  kuma ba akan tatalin arzikiba. Shawar nakarshe ya kamata ya sake yasake yaga katin shi na APC domin yabi bayan Atiku Abubaka a PDP.”

Ya kamata Buhari ya bi shawarar Obasanjo – Isah Muhammed Awo

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Isah Muhammed Awo: “Idan za a duba maganar tsohon shugaban kasa Obasanjo a yi maganar gaskiya ba tare da la’akari da jam’iyyar da mutum yake ciki ba, ya kamata shugaba Buhari ya hakura da sake tsayawa takara a 2019. Da farko ma bisa la’akari da shekarunsa da lafiyarsa, ya kamata ya hakura ya koma gefe a matsayin dattijon kasa mai bayar da shawara kamar yadda sauran tsofaffin shugabannin kasar irinsu Yakubu Gowon da Shagari da Babangida da Abdussalam da sauransu su ka zama. Mu daina tunanin idan ba Buhari ba, babu wanda zai iya gyaran Najeriya saboda shi ma dan Adam ne kamar kowa. Na tabbata ba tare da la’akari da jam’iyya ba, ma’ana a cikin manyan jam’iyyun da muke da su PDP da APC akwai wadanda za su iya dora wa daga inda Buhari ya tsaya ko ma su fi shi iyawa kamar su Makarfi da Atiku da Kwankwaso da El-Rufa’i da dankwambo dukaninsu, idan ka yi la’akari da abubuwa da yawa sun cancanta kuma za su iya rike kasar fiye da Buhari. Don haka ya taimaki lafiyarsa da tsufansa ya hakura da tsayawa takara.

Shawarar Obasanjo ga Buhari ta dace – Hajiya Maryam Umar

Abubakar Rabilu, Gombe

Hajiya Maryam Umar: “A nawa ra’ayin, shawarar da tsohon shugaban Najeriya Obasanjo ya bai wa shugaban kasa Buhari ta dace. Girma ya kama shugaba Muhammadu Buhari, kuma Obasanjo gani ya yi mulkin zai fi da cewa ga mai karancin shekaru, shi ya sa ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata ya koma gida ya zauna saboda ya huta, kwalkwalr shi ma ta samu hutu.

Ya dace ya hakura haka nan – Auwal Differences

Umar Mohammad Gombe, Abuja

Auwal Adamu Differences: “Duk da yake ni masoyin baba Buhari ne na hakika, kuma na fi aminta da gaskiyarsa fiye da kowane dan siyasa a Najeriya, sannan ko yanzu idan ya sake tsayawa takara ba shakka shi zan zaba.

Amma gaskiya na gamsu da wannan shawara ta Obasanjo, a kan Baba Buhari ya hakura daga wannan zango na farko kada ya nemi wa’adi na biyu, domin hakan zai fi jawo masa mutunci da kima a idanun duniya kamar yadda Nelson Mandela tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu ya yi.

Abin da ya fi kamata sh ine ya zakulo wani mutumin kirki mai amana, walau cikin mutanen da ya yi aiki da su a wannan gwamnati ko wani daban, domin ci gaba daga inda ya tsaya wajen dora kasar bisa kyakkyawar turba kamar yadda shi din ya fara.”