Dan Wajalisar Tarayya mai wakiltar Gombe da Kwami da Funakaye a APC daga Jihar Gombe, Hon. Yaya Bauchi Tongo ya ce bai kamata ‘ya’yan jam’iyyarsu ta APC su yi korafin rashin taimaka musu da bai yi ba, yana mai cewa ya shafe shekara biyu yana fadi tashi a kotu dan ganin ya kwato kujerarsa daga hannun Hon. Khamisu Mailantarki.
Hon. Yaya Tongo, ya bayyana haka ne a Gombe a lokacin da ya tara jama’ar mazabarsa don ba su hakuri bisa korafe-korafen da suke yi na cewa bai zuwa kuma bai taimaka mu su.
dan majalisar ya ce akan Hon. Mailantaki ya kamata su yi korafi ba akan sa ba, domin shi ne bai ci zabe ba ya kwace masa kujera wacce sanda ya share shekara biyu yana cin abunda shi ya kamata ya samu dan ya taimake su, amma sai yanzu ya yi nasarar karbar kujerar a wata babbar kotu dake Abuja.
“Kuma a iya sanina a Gombe ta Arewa mu biyu aka zaba, amma ni kadai nake komai, alhalin akwai Sanata amma duk abun da aka yi a wannan yanki ni nake yi bayan kuma duk abunda ake samu a gwamnatance ni daya bisa goma na sanatan nake samu, amma Sanatan baya komai sai ni.
“Don haka dalilin tara wannan taro da ku jama’ar mazabata shi dan in baku hakuri bisa abubuwan da suka faru saboda siyasa na karatowa kuma ina son hadin kan ku shi yasa na zo dan mu fahimci juna. Amma me yasa duk wata dawainiya na siyasa a Arewacin Gombe sai ni kadai nake yi, sannan kuma a rika zargin cewa na guji mutane bayan duk wanda ka ji ya samu mota ko keke ko injin markade ko taimakon aure da sauransu, ni nake yi ba Sanata Bayero ba” in ji shi.
Sai kuma ya yi amfani da wannan dama ya sake bai wa jama’ar ta mazabar tasa hakuri da cewa yanzu ya fita kangin shari’ar da ya yi ta fama a kotuna, dan haka yake godewa Allah yake kuma godewa jama’ar da cewa su kara hakuri bisa abubuwan da suka faru. Daga nan sai ya sake maimaita cewa shi ya san ya yi kuskure, amma dai yana neman jama’a da su yi hakuri za a yi gyara.