✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci a kori Shugaban Hukumar Zabe ta Kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu da wasu manyan jami'an hukumar daga aiki.

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci a kori Shugaban Hukumar Zabe ta Kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu daga aiki.

Obasanjo ya kuma ba da shawarar a sallami wasu manyan jami’an INEC aiki, yana mai kira da a rage tsawon wa’adin shugabancin shugaban hukumar.

Ya yi wannan kira ne a lokcin da yake tsokaci k an zaben shugaban kasa na 2023, wanda ya bayyana mastayin abin takaici.

Don haka ya ba da shawarar a yi cikakken garambawul ga tsarin yadda ake gadanar da zaben kasar.

Ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a taron Zauren Shugabanci na Chinuwa Achebe da ke Jami’ar Yale a kasar Amurka.