Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta hana makiyaya daga kasashen waje shigowa Najeriya domin yin kiwo.
Ya ce ta haka ne kawai za a sami nasarar magance kalubalen tsaron dake addabar kasar.
- CBN na mayar da ’yan Arewa saniyar ware a harkokin kudade – ACF
- Har yanzu El-Rufai bai fahimci batun matsalar rashin tsaro ba — Ganduje
Ganduje ya kuma ce ba daidai ba ne yi wa Fulani kudin goro a matsayin bata-gari, inda ya ce akwai masu yin halastaccen kasuwanci kamar kiwo wadanda kuma suke bukatar tallafi daga masu hannu da shuni domin su ci gaba.
Gwamnan, wanda ke wadannan kalaman yayin wata tattaunawarsa da Gidan Rediyon Faransa (RFI) ranar Alhamis ya kuma caccaki matsayin Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i kan kalubalen tsaro a Arewa maso yamma, inda ya ce Gwamnan sam bai fahimci harkar tsaro ba.