Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta bukaci gwamnatin jihar ta fadada ciyarwar watan azumin Ramadan da take yi kwaryar birni zuwa daukacin kananan hukumomi 23 na jihar.
A zaman majalisa wanda shugabanta Tukur Bala Bodinga ya jagoranta, sun saurari bukatar da dan majalisa mai wakiltar mazabar Tambuwal ta Gabas, Bashir Isa Jabo ya gabatar, inda Kabiru Dauda na mazabar Gada ta Gabas ya goyi bayansa.
Kudirin wanda majalisa ta bayyana cewa abu da ne mai muhimmanci a fadada ciyarwar azumin da gwamnatin ke yi a duk shekara daga kwaryar birnin ya zagaye dukkan kananan hukumomin Sakkwato, duba da halin da ake ciki na matsin rayuwa.
Majalisa na ganin aiwatar da hakan zai samar da saukin rayuwa a cikin jama’ar karkara musamman wadanda ba su da abin da za su ci a lokacin buda baki.
’Yan majalisar gaba daya sun amince gwamnatin jihar ta fadada ciyarwar azumin Ramadan din zuwa dukkan kananan hukumomin jihar Sakkwato.