✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kamata a debi matasa miliyan 5 aikin dan sanda — Basaraken Iwo ga Buhari

Ya ce yin haka zai magance matsalar tsaron Najeriya

Basaraken Oluwo na masarautar Iwo da ke jihar Osun, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi, ya shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya debi matasa miliyan biyar aikin dan sanda matukar yana son kawo karshen matsalar tsaro.

Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Alli Ibrahim ya fitar ranar Lahadi.

A cewar basaraken, ya kamata Buhari ya mayar da Najeriya ‘kasar ’yan sanda’ domin kara inganta harkar tsaronta.

Ya kuma ba da shawarar fito da wani kundin tattara bayanai ta na’ura mai kwakwalwa da zai sa kowanne mazaunin Najeriya ya kasance yana da shaidar bayanansa.

Oluwo na Iwo ya kuma ce, “A matsayinsa na babban kwamandan askarawan Najeriya, ya kamata Buhari ya duba yiwuwar dibar matasa miliyan biyar aikin dan sanda sannan ya inganta albashin dukkan jami’an tsaro.

“Najeriya, duk da tana da yawan mutanen da bai gaza miliyan 250 ba, amma kwata-kwata yawan ’yan sandanta bai wuce 300,000 ba.

“Kari a kan haka kuma, ya kamata a inganta harkar adana bayanan mutane ta na’ura mai kwakwalwa ta yadda ’yan sanda za su sami damar tattara bayanan mutane ko da kuwa a ina suke.

“Dole a fito da hanyar tilasta wa mutane dokar yawo da katin shaida. Idan aka yi haka, masu aikata laifi da sauran ’yan bindiga za su sha wahalar zirga-zirga a tsakaninmu, inji basaraken.