’Yan bindiga a Jihar Zamfara, karkashin jagorancin wani kasurgumin shugabansu, Turji, sun kai hari kauyuka da dama tare da sace matafiya a Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar.
An dai fara kai farmakin ne ranar Juma’a a wani mataki mai kama da na ramuwar gayya saboda kama mahaifin Turji da jami’an tsaro suka yi.
- An kama boka da kokon kan mutum a Kuros Riba
- Ambaliyar ruwa: mutum 100 sun mutu, sama da 1,000 sun bata a Jamus
Aminiya ta gano cewa akalla mutum 150 ne aka yi awon gaba da su a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Wasu majiyoyi daga yankin sun ce jami’an tsaro sun kama mahaifin Turjin ne a Kano, kimanin makonni biyu da suka gabata, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.
Kauyukan da aka kai wa farmakin ranar Juma’a su ne Kurya da Keta da Kware da Badarawa da Marisuwa da kuma Maberaya.
Rahotanni sun ce baya ga kai farmakin, ’yan bindigar sun yi garkuwa da matafiya masu yawa a kan babbar hanyar Gusau zuwa Sakkwato.
Jagoran ’yan bindigan dai ya lashi takobin cewar matukar ba a saki mahaifin nasa ya yi bikin Babbar Sallah a gida ba, to ba shakka shi ma zai tabbatar iyalai da yawa ba su yi ta tare da nasu iyalan ba.
“An kira shi a waya yayin wani taro tsakanin mazauna yankunan da jami’an tsaro inda ya yi korafi kan kama mahaifin nasa; Ya shaida wa taron cewa shi ne dan ta’adda kuma an san inda yake, saboda haka babu dalilin a kama mahaifinsa,” inji wata majiya da ta halarci taron a wancan lokacin.
Kazalika, wata majiyar wacce ta tattauna da wakilinmu ta ce Turji ya kuma aike da sakon gargadi ga kauyukan da yake shiri da su a yankin da su tattara su bar garuruwan.
“Yaranshi sun kuma je garin Shinkafi ranar Juma’a da dare inda suka sace mata biyar,” inji majiyar.
Wani mazaunin Shinkafin, Mohammed Sani, ya shaida wa Aminiya cewa wani gurneti da aka jefa yayin harin ya lalata wani sashe na fadar sarkin garin.
Sai dai da muka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa kiran wakilinmu ta waya ba.