Wadansu likitoci sun yi tiyatar ciro buroshi daga cikin wani mutum bayan ya hadiye shi a lokacin da yake kokarin goge cikin makogwaronsa.
Buroshin da likitocin suka ciro ya kai tsawon santimita 19 kuma an yi masa tiyatar ce cikin awa 24 da hadiye buroshin. A cewar likitocin
dadewar buroshin a cikin mutumin ka iya sanadin mutuwarsa.
- A kokarin rage kiba ta hadiye roba mai tsawon santimita 30
- Kokarin ciro kayar kifi a makogwaro ya sa ta hadiye cokali
Mara lafiyar wanda aka sakaya sunansa mai shekara 39, ya gamu da tsautsayi ne lokacin da yake goge hakoransa a ranar 15 ga Satumban bana, sai buroshin ya wuce cikinsa, daga nan aka kai shi asibiti mafi kusa, sai asibitin suka tura shi zuwa wani asibiti mai nisan da kilomita 100 daga garin marar lafiyar.
Bayan yin hoton cikin (X-ray) sai gwajin ya nuna buroshin ba ya cikin makogwaronsa, inda likitocin suka gano cewa, ya hadiye buroshin ne kuma yana cikinsa.
Hakan ya sa aka yi tiyata aka ciro buroshin. Mutumin ya ci gaba da jinya a asibitin bayan yi masa tiyata, daga bisani aka sallame shi bayan ’yan kwanaki.
Babban likitan tiyata na babban asibitin Bakin Pertin da ke garin Pradesh, a kasar Indiya, Dokta Bomni Tayeng ya ce, “An kai mutumin asibiti mai zaman kansa da ke garin Pasighat hedkwatar jihar Arunachal
Pradesh a Indiya, daga nan aka wuce da shi babban asibitin aka yi masa tiyata bayan binciken da likitoci da suka yi, ya nuna cewa, yana buqatar a yi masa tiyata, wadda aka yi a ranar 16 ga Satumba, 2020.
Da farko an fara duba cikin makogwaronsa ne ba a samu buroshin ba, sai a cikinsa aka samu.”
Dokta Bomni ya qara da cewa, mutumin yana cikin qoshin lafiya bayan yi masa tiyatar inda aka yi nasarar ciro buroshin, sai dai yana fama da wani karamin ciwo a saman cikinsa.
A cewar likitan an gano gurbin da buroshin yake ne bayan daukar hoton cikinsa ta hanyar amfani da X-ray daga nan aka yi amfani da na’ura aka fitar da abin da ya hadiye.
An yi masa tiyatar cire buroshin ne ta hanyar yanka wani vangare na cikinsa, hakan ya dauki kusan mintuna 30.
Kwana guda da yin tiyatar ya fara shan magani sannan ya fara samun sauqi, bayan jinyar an sallame shi a ranar 21 ga Satumban da ya gabata.