✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya gurfana a gaban kotu bisa zargin damfara da sunan canjin kudade

Wata Kotun majistare dake zamanta a unguwar Gyadi-gyadi a Kano ta fara sauraron wata kara inda ake zargin wani

Wata Kotun majistare dake zamanta a unguwar Gyadi-gyadi a Kano ta fara sauraron wata kara inda ake zargin wani mutum da laifin damfarar abokin huldarsa kudi har Naira miliyan uku.
An dai gurfanar da mutumin mai suna Lurwanu Tasi’u ne bisa zargin damfarar wani mutum da nufin cewa zai ba shi Dalar Amurka ta zunzurutun kudin.
Tun da farko dai Lurwanu sun kulla wata yarjejeniya da mutumin kan za su yi musayar Naira da Dalar Amurka, sai suka shirya komai a tsare a tsakaninsu kan shi Lurwanun zai ba wa mutumin Daloli shi kuma mutumin zai ba shi Nairar miliyan uku.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya bukaci mutumin da ya kai kudin karkashin wata bishiya a can cikin wani surkukin daji, inda daga nan shi kuma ya dauki numfashin mutumin ya zagaye ya kwashe kudaden.
Yayin zaman kotun, bayan karantawa Lurwanun laifin da ake zarginsa da aikatawa, nan take ya musanta tare da kin yarda da aikatawa.
Daga nan ne kuma lauyansa Hamza Sani Bawa, ya bukaci  kotun da ta bayar da belin Lurwanu.
Daga nan ne mai shari’a Auwal Yusuf, ya dage zaman Kotun zuwa ranar 5 ga watan Janairun 2021 a matsayin domin ci gaba da sauraron karar.
Sai dai lauyoyin mai gabatar da karar a gaban kotun sun ki su ce uffan akan shari’ar.