✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 14 sun rasu, gidaje 50 sun salwanta a ambaliyar Gombe

Duk da karamar hukumar Funakaye ba ta cikin kananan hukumomin da ake da rahoton samun ambaliyar, sai gashi a ranar 29 ga watan Yuli an…

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Gombe SEMA ta ce ambaliyar ruwa a bana an janyo asarar rayuka 14 da gidaje sama da 50, tare da shafar kimanin mutane 600 a fadin jihar.

Darakta a hukumar ta SEMA kuma mai kula da bada agajin gaggawa, Mihammad Garba, ne ya bayyana cewa ambaliyar tafi shafar kananan hukumomi 7 cikin 11 da ke jihar.

Muhammad Garba, ya ce ambaliyar ta fi shafar kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba da Kwami da Dukku da Kaltungo da kuma Shongom.

Sai dai a cewarsa, duk da karamar hukumar Funakaye ba ta cikin kananan hukumomin da ake da rahoton samun ambaliyar, sai gashi a ranar 29 ga watan Yuli an samu ambaliya da ta halaka rayuka 14 da gidaje fiye da 50 da ta shafi magidanta fiye da 600 inda ruwa ya malale garin Bagoja da wasu makwabtan ta baki daya.

Ya ce a lokacin da ambaliyar ta faru, sun sanar da gwamnatin jihar inda nan take gwamnan, duk da baya gari, ya umarci ma’aikatar kula da muhalli, suka hadu da SEMA suka je garin suka duba sannan suka bada tallafi.

Muhammad Garba, ya ce sun bai wa al’ummar da Aambaliyar ta shafa tallafin kayan abinci da na aikin gida da kuma magunguna.

Daga nan sai ya ja hankalin jama’a da cewa su dinga amfani da fadakarwar da ake musu na daukar matakan kariya kafin saukar damina kamar da sa bishiya da sauransu don samun saukin ambaliya.