Wasu rahotanni daga Bandar Abbas, babban birnin kasar Iran, sun bayyana yadda wasu mutum takwas suka mutu bayan kwankwadar barasa.
Tuni aka kwantar da mutum 51 a asibiti sakamakon shan barasar da ake zargin akwai guba a cikinta.
Wata jami’ar lafiya a birnin Dokta Fatemeh Nowruzian ta shaida wa manema labarai cewar mutum 17 daga cikinsu na cikin wani mawuyacin hali.
Har wa yau, ta shaida cewar mutum 30 da ake yi wa wankin-koda, don ceto rayuwarsu.
‘Yan sanda sun ce sun kama mutum takwas bisa zargin yin barasar da ake zargin akwai guba a cikinta da kuma raba ta ga jama’a.
Kasar Iran ta haramta yin barasa da sayar da ita ko kuma shan ta, amma an sassauta dokar ga wadanda ba musulmai ba.
Ana yi wa dukkan musulmin da aka samu da lafin shan barasa bulala 80 a kasar.
Ya zuwa yanzu jami’an tsaro a kasar ba su bayyana musababbin abin da ya hallaka mutum takwas din ba, amma ana zargin barasar na dauke da sinadarin methanol da ya wuce kima a cikinta.
Ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar da cewar a watan Afrilun 2020, mutane 500 ne suka mutu sannan wasu 5,000 kuma aka yi musu wankin-koda sakamakon kwankwadar barasa cikin watanni uku.