Wata Kotun majistare dake zamanta a unguwar Gyadi-gyadi a Kano ta fara sauraron wata kara inda ake zargin wani mutum da laifin damfarar abokin huldarsa kudi har Naira miliyan uku.
An dai gurfanar da mutumin mai suna Lurwanu Tasi’u ne bisa zargin damfarar wani mutum da nufin cewa zai ba shi Dalar Amurka ta zunzurutun kudin.
- Kisan Zabarmari: Majalisa ta bukaci Buhari ya kori Hafsoshin Tsaro
- Kashe-kashe: Shaikh Gumi ya bukaci Buhari ya yi murabus
- Budurwa ta tura wa saurayinta ’yan fashi a Kano
Tun da farko dai Lurwanu sun kulla wata yarjejeniya da mutumin kan za su yi musayar Naira da Dalar Amurka, sai suka shirya komai a tsare a tsakaninsu kan shi Lurwanun zai ba wa mutumin Daloli shi kuma mutumin zai ba shi Nairar miliyan uku.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya bukaci mutumin da ya kai kudin karkashin wata bishiya a can cikin wani surkukin daji, inda daga nan shi kuma ya dauki numfashin mutumin ya zagaye ya kwashe kudaden.
Yayin zaman kotun, bayan karantawa Lurwanun laifin da ake zarginsa da aikatawa, nan take ya musanta tare da kin yarda da aikatawa.
Daga nan ne kuma lauyansa Hamza Sani Bawa, ya bukaci kotun da ta bayar da belin Lurwanu.
Daga nan ne mai shari’a Auwal Yusuf, ya dage zaman Kotun zuwa ranar 5 ga watan Janairun 2021 a matsayin domin ci gaba da sauraron karar.
Sai dai lauyoyin mai gabatar da karar a gaban kotun sun ki su ce uffan akan shari’ar.