✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya gargadi ’yan fansho su guji bai wa ma’aikatansa cin hanci

Shugaban Hukumar Biyan Fansho ta Jihar Jigawa, Alhaji Sulaiman Adamu Kiyawa ya gargadi ’yan fansho a jihar su guji bai wa ma’aikatan hukumarsa na goro…

Shugaban Hukumar Biyan Fansho ta Jihar Jigawa, Alhaji Sulaiman Adamu Kiyawa ya gargadi ’yan fansho a jihar su guji bai wa ma’aikatan hukumarsa na goro kuma su tona asirin duk ma’aikacin da ya bukaci kudi a wajensu kafin ya yi musu wani abu da suke da bukata.

Alhaji Sulaiman Kiyawa ya ce suna da masaniya a kan wadansu batagari da suke zagayawa a jihar suna damfarar wadanda suka bar aiki cewa za su taimaka musu wajen samun kudadensu na fansho cikin sauki ko samar musu littafin karbar fansho idan nasu ya cika ko ya bata. 

Ya roki ’yan fanshon su hanzarta sanar da ’yan sanda ko hukumar kan irin wadannan mutane domin daukar mataki a kansu.

Shugaban ya fadi haka ne makon jiya lokacin da ya kira taron manema labarai a ofishinsa, inda ya kuma bukaci manema labarai su rika fadakar da ’yan fanshon kan su yi hattara da wadanda suke yin mu’amala da su a bankuna domin sun samu labarin akwai wadanda suke zuwa bankuna suna cutar da mutane ta hanyar cewa za su taimaka wa mutum idan suka ga ba zai iya cire kudinsa daga na’urar ATM ba, inda suke amfani da damar su sauya wa mutanen lambar sirri ta katin ATM su sace musu kudi daga baya.

Alhaji Sulaiman Kiyawa ya ce gwamnatin jihar ta biya wadanda suka bar aiki da wadanda suka rasu da iyalan wadanda suka bar aiki amma ba su kai shekara biyar ba da barin aiki ba suka rasu su 339 hakkokinsu.

Ya ce gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 461 da dubu 450 da 509, domin biyan wadanda abin ya shafa kudadensu, kuma ya ce wadanda suka bar aiki mutum 207, an ware Naira miliyan 263 da 994 da 268 don biyansu hakkokinsu, yayin da wadanda suka rasu a bakin aiki mutum 94 aka ware Naira miliyan 177 da dubu 604 da 762 don biyansu sai wadanda suka rasu bayan sun fara karbar fansho mutum 33 gwamnatin ta kashe Naira miliyan 18 da dubu 938 da 91 don biyansu hakkokinsu. Ya ce sai kuma wadanda suka bar aiki amma shekarunsu na ritaya ba su kai ba ko kuma an yi musu ritaya saboda shekarunsu na haihuwa sun wuce lokacin aiki kuma sun ba da kashi 8 cikin 100 na kudin hadakar fansho su  4 ne an ware Naira dubu 913 da 387 don biyansu hakkokinsu.