✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace mu rika martaba addininmu a waka – Khalid D-Guy

Khalid Gambo, wanda ak fi sani da D-Guy yana daya daga cikin mawakan Hip-pop a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda wakokin…

Khalid Gambo, wanda ak fi sani da D-Guy yana daya daga cikin mawakan Hip-pop a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda wakokin zamani na Hausa (Hip-pop) suka samu karbuwa a wuirn jama’a da kuma yadda yake ganin za a ciyar da harkar gaba:

Za mu so jin tarihin rayuwarka a takaice.

Ni sunana Khalid Gambo Mahmud, sai dai an fi sanina da D-guy. An haife ni a 1982 a Kwanar Dumawa a karamar Hukumar Minjiibir. Bayan rasuwar mahaifina ne a 1990 na dawo da zama unguwar Tudun Bojuwa cikin birnin Kano. A nan na yi karatun firamare, da na gama sai na tafi wata makarantar sakandare da ke Jigawa. Bayan na kammala karamar sakandare sai na tafi makarantar Army Day, inda na kammala babban sakandare a can.
Daga nana ban samu damar karo karatu ba sai na shiga harkar kasuwanci. Na yi sana’o’i da dama da suka hada da rinin kamfala da sayar da maganin gargajiya da sauransu. Haka kuma na yi sana’ar sayar da atamfofi a Kasuwar Kantin Kwari. Daga baya kuma sai na koyi aikin kanikanci. A yanzu haka ina aiki da wani kamfani a Challawa a Jihar Kano, a matsayin daya daga cikin kanikawan kamfanin.
Batun iyali kuma kwanan nan na yi aure ina zaune a unguwar Gaida a yankin karamar Hukumar Gwale.
Ya aka yi ka shiga harkar waka kuma yaushe ka fara?
Na kasance tun ina yaro nake sha’awar waka. Da na girma kuma sai na fara rubutawa kuma har ina rerawa da kaina. Lokacin da na fara waka sosai shi ne a 2000, inda muka yi wata waka tare da su Mas’ud Riders (Wakar Fati Inda Rai). Ba zan iya cewa ga wanda ya koya mini waka ba, tashi na yi na ga ina yi, sai dai da na shiga harkar sosai nakan sami masu ba ni shawarwari a harkar da sauransu.
A kan me ka fi yin wakokinka?
Duk abin da ya burge ni nakan iya yi masa waka. Amma yawancin jigon wakokina a kan abin da ya shafi addini ne ko soyayya, musamman idan mace ta ki ni ko ta ki wani na kusa da ni. Sai dai kamar sauran ’yan uwana mawakan Hip-pop ba na yin waka a wajen biki. Haka kuma wakokin sukan bambanta ta hanyar yin amfani da kafiya. Hakan ya jawo har abokan sana’ata na kira na da lakanin ‘Sarkin kafiya.’ Haka kuma ina iya canza murya a wakokina.
Zuwa yanzu albam din waka nawa ka fitar kasuwa?
Duk da cewa har yanzu ba ni da albam nawa na kaina amma nakan fito a cikin bidiyon wakokin abokan sana’ata. Haka kuma ina da faya-fayan da na sanya wakokina a ciki kusan guda ashirin. Sai dai in sha Allahu nan gaba zan yi albam dina da zarar na kammala wasu abubuwa da suka sha mini kai.
Kuna da kungiya ta mawakan Hip-pop?
A da mun kafa kungiyoyi da dama, kamar su Mecon Music, sai dai wacce ta fi yin shahara ita ce wacce muke kira boice of African (Muryar Afirika), inda muka hadu da wasu mawakan irinsu Mas’ud Kano Riders da su Baba G, irin su CK da sauransu, daga baya kuma sai ita ma wannan kungiyar ta watse. Sai dai duk da cewar a yanzu ba mu da wata tsayayyar kungiya amma mu mawakan Hip-pop wato, muna da hadin kai sosai a tsakaninmu. A yanzu haka ma muna shirye-shiryen kafa kungiya mai karfi don har mun kai matakin an raba mana fom don mu
cika. Muna fatan ta zama sanadiyyar haduwar kai tsakaninmu tare da ciyar da sana’armu gaba.
Yawancin mutane na yi muku kallon wasu mutane masu kwaiwkayon Turawa ta fuskar sanya sutura da kuma wakar kanta, me za ka ce a kan hakan?
Babu shakka a da mutane na yi mana wannan mummunar fahimtar amma alhamdu lillahi, a yanzu abin ya ragu sosai. Mun fara samun karbuwa a wajen jama’a. Hakan ya faru ne sakamkon fahimta da mutanen suka yi game da yadda muke amfani da salon wakokinmu wajen fadakar da al’umma kan abubuwan da suka shafi addini da rayuwa gaba daya. A yanzu haka a gidajen rediyon Jihar Kano ana sanya wakokinmu. A haka mutane sun fahimci inda muka sa gaba, muna ganin ci gaban wannan harka nan da
’yan shekaru masu zuwa idan Allah Ya yarda. Haka kuma batun sanya sutura ba wai kawai sai da irin suturun Turawa muke yin wakokinmu ba, mukan yi da dogayen kaya na Huasawa. Ya danganta da abin da mutum yake so. Idan kika dauki kamar ni misali, ba zan damu ko jin kunya don an sanya wakokina a gaban iyayena ko ’ya’yana ba. Ni ba zan damu don dana ya gaje ni ba.
Wane kira kake da shi ga gwamnati?
Muna kira ga gwamnati da ta rika tallafa mana kasancewarmu mu ma wannan harka mun dauke ta a matsayin sana’ar da muke dogaro da ita. Haka kuma muna neman gwamnati da ta ba mu dama mu rika gudanar da wasan dabe, inda za mu samu fili mu yi wakokinmu, masoyanmu su zo su kalle mu a zahiri. Duk da cewar hajarmu ce za mu kasa, amma mun tabbata gwamnati za ta sami kudin shiga daga ciki. Idan za mu gudanar da irin wannan wasan za mu so gwamnati ta ba mu ’yan sanda da jami’an Hisba don tabbatar da tsaro da kuma hana faruwar abubuwa irin na badala ko shaye-shaye da sauransu a wurin.
Wane kira kake da shi ga abokan sana’arka?
Duk da cewa akwai kyakkyawar alaka a tskaanimu, ina kara yin kira gare mu da mu zama tsintsiya madaurinmu daya. Mu hada kanmu, kada mu yarda wasu na ciki ko na waje su rika kai-kawo da maganganu a tsakaninmu. Abu na gaba shi ne, akwai bukatar mu rika kokarin kare addininmu da al’adarmu a wakokinmu. Mu san irin kalaman da za mu rika amfaniu da su a cikin wakokinmu. A yanzu haka wani dag cikin mawakanmu yana nan yana ta kokarin wayar da kanmu wajen ganin mun daina sanya kalmomin zagi a wakokinmu.