Ana zargin wani magidanci da soka wa matarsa wuka ya kashe ta a yankin Korinda na Karamar Hukumar Konshisha da ke Jihar Binuwai.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta shaida wa wakiliyarmu cewa ma’auratan sun samu wata takaddama ce a ranar Talata, inda a garin haka, mijin ya soka wa matar wani abu mai kaifi kamar wuka, ta ce ga garinku nan.
- Jami’an tsaro sun kama AK-47 guda 150 a gidan dan ta’adda a Neja
- An tsare ta a kurkuku kan kisan jiririn kishiyarta
- An gurfanar da dan siyasar Kano a kotu kan barazanar dukan malamin addini
Dai da ce zuwa lokacin ba su da cikakken bayani, suna jiran DPO na yankin Konshisha ya turo rahotonsa domin samun karin bayani kan aihinin abin da ya faru.
Wasu mazauna yankin na Korinya sun bayyana suna marigayiyar a matsayin Mngusunun.