✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Xi Jinping ya sake zama Shugaban China a wa’adi na uku

Taron kolin jam'iyyar Kwamisancin a China ya zabi shugaba Xi Jinping a wani sabon wa'adi na uku.

A karon farko cikin tarihi shugaban China Xi Jinping zai dore a wa’adi na uku na mulkin kasar bayan da babban taron jam’iyyar Kwaminisanci ya sake zabar shi a matsayin shugaba.

Hakan na nufin Mista Xi ya zama shugaba mafi karfin fada-a-ji tun da Mao Zedong ya mulki kasar.

A halin yanzu dai Jam’iyyar Kwaminisanci ta kasar ta tabbatar da shi a matsayin Babban Sakataren jam’iyyar wanda hakan ke nufin a watan Maris mai zuwa yana da tabbacin dorawa a kan mulkin kasar na wasu shekaru biyar.

Kafin a kawo wannan matakin, tuni manyan kusoshin jam’iyyar suka bayyana goyon bayansu ga tsawaita wa’adin mulkin Mista Xi, baya ga amincewa da suka yi ga wasu sauye-sauye masu yawa da suka tilasta wa wasu manyan jami’ai ajiye mukamansu

Bayan Shugaba Jinping, taron ya kuma zabi wasu da ake ganin na hannun damansa hudu a mukamai mabanbanta don tafiyar da harkokin jam’iyyar da ma mulki.

A cikin watan Maris na 2023 ake sa ran taron kwamitin zartarwar jam’iyyar Kwamisancin zai zabi Li Qiang shugaban Shanghai a matsayin sabon firaminista inda zai maye gurbin Li Keqiang.

Wasu da suka hada da Ding Xuexiang da Li Xi shugaban jam’iyyar a lardin Guangdong na daga cikin wadanda aka nada a manyan mukamai na tafiyar harkokin mulki.