Kasa da sa’o’i 48 bayan Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (TCN) ta dawo da hasken wutar lantarki a birnin Miaduguri na jihar Borno, ’yan ta’addan Boko Haram sun sake datse wani sashe na hanyar wutar.
Wani babban jami’in hukumar ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya a wani rubutaccen sako da yammacin Asabar.
- An karrama kamfanin giya a matsayin wanda ya fi kowanne biyan haraji a Kaduna
- Fashewar bam ta tarwatsa masu zabe a Abiya
A cikin sakon dai jami’in ya ce, “Bayan dukkan kokarin da muka yi na dawo da wutar lantarki ga Maiduguri, ’yan ta’addan sun sake tayar da bam a jikin wata na’urar wutar lantarkin dake kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri mai karfin KVA 330 da misalin karfe 5:56 na safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Maris 2021.”
A ranar Larabar da ta gabata dai an yi ta murna a Maiduguri bayan Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Shiyyar Yola (YEDC) ya dawo da wutar bayan kokarin hukumar ta TCN.
Birnin dai ya shafe kusan watanni biyu a cikin duhu tun bayan da ’yan Boko Haram din suka kai hari a kan wata na’urar rarraba wutar dake garin Jakana a ranar 26 ga watan Janairun 2021.
Ko a lokacin da injiniyoyin TCN ke aikin dawo da wutar a kwanakin baya dai sai da motarsu ta taka wata nakiya da ’yan Boko Haram din suka binne da nufin hana su gyaran.