✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ta yi ajalin mutum 4 a Kaduna

W

An samu wani iftila’i a ƙauyen Kwarau da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, biyo bayan mutuwar wasu mutanen ƙauyen huɗu da wayar wutar lantarki ta kama.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:40 na safiyar ranar Asabar yayin da yawancin mazauna garin ke barci a gida.

Har yanzu dai ba a tabbatar da ainihin musabbabin faruwar lamarin ba, amma wasu mazauna yankin sun danganta lamarin da wata wayar wutar lantarki da ta faɗa kan tiransfoma.

Aminiya ta ruwaito cewa, wayar wutar da ta faɗa kan tiransfoma ce ta yi sanadin ƙaruwar ƙarfin wutar a gidaje da dama a ƙaramar hukumar.

Wani mazaunin garin Lawal Ismail ya bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da suka haɗa da Malam Saminu da Sani da Labi da wata yarinya budurwa, yayin da waɗanda suka jikkata ke jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Mohammed Rabi’u Kwarau, Kansila mai wakiltar mazabar Kwarau, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutane huɗu sun mutu, wasu huɗu kuma suna jinya.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi, ya kuma buƙaci hukumomi da su magance matsalolin wutar lantarki da ake fama da su a tsakanin unguwannin, yana mai cewa ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan matsalar wutar lantarki ba.

“Mun yi matukar bakin ciki da wannan iftila’in da ya yi sanadin mutuwar mutanenmu huɗu—maza uku da wata yarinya.

“Babbar hanyar raba wutar ce ta janyo ƙaruwar ƙarfin wutar lantarki a mafi yawan gidajen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutanen,” in ji shi.