✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar Kaikayi: Nazarin littafin Tarkon Mut’a (2)

Sunan Littafi: Tarkon Mut’a (Wasan Kwaikwayo) Sunan Marubuci: Bashir Yahuza Malumfashi Shekarar Wallafa: 2019 Kamfanin Wallafa: Gizago Publishing Enterprises Yawan Shafuka: 100 Lambar ISBN: 978-2149-99-3…

Sunan Littafi: Tarkon Mut’a (Wasan Kwaikwayo)

Sunan Marubuci: Bashir Yahuza Malumfashi

Shekarar Wallafa: 2019

Kamfanin Wallafa: Gizago Publishing Enterprises

Yawan Shafuka: 100

Lambar ISBN: 978-2149-99-3

Farashi: Naira 500

 

Kashegari Nana ta yi wa iyayenta karyar cewa ana neman su a makaranta don karbar sakamakon jarabawarsu, aka ba ta kudin mota ta fita. Duk da yanke shawarar biye wa Dandangi don a zubar da cikin, zuciyarta na kai-kawo kan wannan lamari, inda cikin waya da suka yi da shi ta rika yi masa tambayoyi kan abin da ya fada mata tun fari game da auren Mut’a, amma a aikace ta ga sabanin haka.

“…Ka kawo mani wata hujja da ke cewa ai a akidar Shi’a, dan da aka haifa daga Auren Mut’a ya fi albarka. Tsakani da Allah ba mu yi haka da kai ba?

“To ka tuna fa Auren Mut’a muka yi, muka samu wannan cikin da ke jikina dan wata uku. Idan dai har ka yarda da hujjojin halalta Auren Mut’a, idan dai har ka yarda cewa dan da aka samu daga Mut’a ya fi albarka, to me ya sa za ka ce mu zubar da cikin nan? Me ya sa ba za mu bijirar da abin da za mu haifa ga iyayenmu ba?” (shafi na 66).

A motar da Nana ta shiga daga Dutsin-ma zuwa Katsina ma, sai da aka kai ruwa rana da wani fasinja dan Shi’a, inda direban motar ya sanya wa’azin ’yan Sunna, dan Shi’ar kuma ya ce sai dai a sanya wani daban, al’amarin da ya kai har sai da suka tsaya, daga karshe shi dan Shi’ar da ke zaune a gaban motar ya koma mazaunin baya.

A haka dai har motar ta isa Katsina Nana ta sauka, ta kira Dandangi ya kwatanta mata asibitin, inda yake can cikin tsumayin ta. Ta hau acaba ta isa suka karasa. Nana ta zaga makewayi, sai ta ji ma’aikatan asibitin na tsegumin wata tangarda da aka samu kan wani aikin zubar da ciki da liikitan ya yi.

A tsorace Nana ta fito daga makewayin. Tana isa zauren karbar baki na asibitin, ta tarar da wurin a hautsine, sakamakon wasu matasa majiya karfi da suka cika wurin dauke da makamai suna neman likitan don kaddamar masa.

“Wuyyii! Huuuu!! Tun da ka kashe mana kanwa, yau kemis din nan ya tashi aiki!!! (ya fara watsa fetur, zauren duk ya dauki hautsini da hayaniya)

“Wuyyiii! Ku buge! Ku kone!!! (shafi na 89-90).

Wurin ya kama ta wuta. Hayaki ya turnuke ko’ina, Nana da Dandangi suka fita a guje. Wajen gudun ne mota ta banke Dandangi, ta murje masa kafafunsa biyu ta wuce. Ita kuma Nana ta je tsallaka wata babbar kwata, kafarta ta zame ta fadi har cikinta ya bugu, nan take jini ya yanke mata (cikin da take dauke da shi ya zube). Shi kuwa Dandangi kafafunsa suka dagargaje, sai yanke su aka yi. Nana kuma ta koma gida ta nemi gafarar iyayenta, suka yafe mata.

 

Salo:

Salon wannan wasan kwaikwayo na gaba daya mai armashi ne, kasancewar yadda aka kukkulla zaren labarin zai yi ta jan mai karatu cikin zakuwa don jin yadda labarin zai kare.

An yi amfani da daidaitacciyar Hausa wajen rubuta littafin, in ban da wasu wurare da aka jefa wasu kalmomi na karin harshe na shiyya.

Haka nan akwai ’yan kura-kuren ka’idojin rubutu, musamman a can karshen littafin. Ta yiwu wajen tacewa aka yi wa abin ’yar sauri, ya zamo ba a ankara da su ba. Ga wasu daga ciki:

Ban sanku ba, maimakon        ban san ku ba, a shafi na 37.

Saida safe, maimakon            sai da safe, a shafi na 62.

Sai anjima, maimakon           sai an jima, a shafi na 81.

Bazan, maimakon ba zan, a shafi na 62.

Maida, maimakon  mai da, ashafi na 82.

Kiranta, maimakon                kiran ta, a shafi na 81.

Da ma, maimakon da ma, a shafi na 80.

Haka kuma bakin Alhamza /’/ bai fita ba a duk rubutun littafin. Ta yiwu an samu tangardar na’urar da aka buga littafin da ita ne.

Littafin cike yake da kamanci irin na tamka, har ma da na fifiko da aka kawata zantukan da su. Ga misalan wasu daga ciki:

“Gardama kamar makahon jaki.” (shafi na 3).

“Kullum suna cikin bakaken kaya, kamar wadanda aka yi wa gorin dinya.” (shafi na 20).

“A tsaye kikam kamar wacce ta hadiyi tabarya.” (Shafi na 34).

“Rashin nutsuwa kamar kifi a fako.” (shafi na 35).

“Sharrinsa ya fi dafin bakin kumurci.”      (Shafi na 35).

“Cikin huci kamar kububuwa.” (Shafi na 72).

Haka kuma littafin tumbatse yake da dumbin karin maganganu da suka kara wa zantukan dandano, kamar:

“Ban ga hadin kaska da kifi ba.” (Shafi na 2).

“Wahaba, toshi bayan salla.” (shafi na 5).

“Tarihin (labarin) kanzon kurege.” (Shafi na 16).

“Karya linzamin shaidan, mai sarrafa ta sai dan bogi (Shafi na 32).

“Ina zakara za shi da kayan taiki?” (shafi na 44).

“Ranar wanka ba a boyon cibi. (shafi na 5 da na 54).

Akwai kalmomin fannu, wato kalmomi masu dangantaka da jigon littafin masu yawa da aka yi amfani da su, kamar:

Takiyya/balulluba, shafi na 8.

Mut’a, shafi na 42, da wasu wurare da dama.

Rafilawa (shi’a), shafi na 10.

Firkoki, shafi na 12.

‘Yan Hurras, shafi na 19.

Fudiyya, shafi na 30.

Ilahi! shafi na 31.

Ya Hussain! shafi na 32.

Ya Fatima! shafi na 32.

Mukabala, shafi na 54.

Auren da’iman, shafi na 53.

Alka (halka) hafi na 28.

Akwai kuma Hadisan Annabi da aka kafa hujja da su a wasu wurare, kamar shafi na 35, 36 da na 38.

Kasancewar jigon littafin ya shafi addini, akwai ararrun kalmomin Larabci masu yawa, kamar: shubuhohi (shafi na 13), Istidraji (shafi na 29), Ibtila’i (shafi na 61), Ijara, lada – shafi 77), haiba (shafi 77), da sauransu.

Akwai kuma ararrun kalmomin Turanci irin su Lasi/lasisi (shafi na 53), One chance (shafi na 51), Halo! (shafi na 60 da 63), da Hostel (shafi na 47).

Kasancewar marubucin littafin sha’iri ne, ya kawata littafin da wasu wakoki biyu, daya wadda shi ne ya rubuta mai taken “Uwar Muminai Nana A’isha” (shafi na 81-82), dayar kuma wallafar Malam Abba Idris Adamu Amizat kamar yadda ya ruwaito mana, mai taken “Auren Mut’a Jidali” (shafi na 78-80).

 

Tauraro

Tauraron wannan wasan kwaikwayo ita ce Nana, duk da kasancewar akwai wasu manyan taurarin da suka taka babbar rawa cikin wasan, kamar abokin Mut’arta Dandangi.

Da Nana aka fara wasan tun a fitowar farko, inda aka nuna yadda ta yi ta haraswa ba kakkautawa. Duk kuma abubuwan da suka wakana cikin wasan kan matsalar da ta samu kanta ciki ne, wato rungumar akidar Shi’a, da fadawa tarkon Auren Mut’a. Haka kuma da Nana aka yi fitowar karshe ta wasan, inda aka nuna yadda faduwar da ta yi har cikinta ya bugu, ta zamo sanadiyyar zubewar cikin shegen da take dauke da shi.

 

Halayen Wasu ’Yan Wasa

Kamar yadda aka nuna a cikin wasan:

Dandangi

Shi ne tauraro na biyu bayan babbar tauraruwar wasan. Matashi ne da ya yi kaurin suna wajen bin tafarkin Shi’a. Kwararre wajen iya jawo hankalin wasu zuwa akidarsa musamman ’yan mata, wadanda yakan yi amfani da lasisin Auren Mut’a yana samun biyan bukatarsa ta sha’awa daga gare su, su kuma yana barin su cikin kaico yayin da suka farga. Dubi irin abin da ya ce wa Nana a farkon haduwarsu:

“Wannan gaskiya ne. Amma idan ba za ki damu ba, ki ba ni lambar wayarki, sai mu ci gaba da gaisawar zumunci. Kin ga dai ga shi mun fito gari daya, babu mamaki mu amfani juna.” (Shafi na 6).

 

Katume

Ita ce mahaifiyar Nana. Dattijuwa mai zurfin ciki. Duk da ta fahimci abin da Nana take ciki daga abin da ta sani na canzawar dabi’unta, amma ba ta nuna mata hakan ba. Haka ma har zuwa lokacin da suka gano alamun cewa ta shiga Shi’a, ba ta fada wa mahaifin Nana ba. Dubi irin yadda ta bayyana masa larurar da Nana ke fama da ita:

“To dazu dai da hantsi zazzabi ya rufe ta har da amai. Ta ce Maleriya ce. Na so in kira ka ta waya ka a kai ta asibiti, ta ce in bari ta sha magani. Amma tun dazu tana daki kwance. Ni hankalina ya tashi wallahi, domin duk ciwon da aka ce ya hada da amai ko gudawa abin tsoro ne.” (shafi na 23).

 

Baban Nana

Shi ne mahaifin Nana. Nagartaccen mutum mai kula da addini ta hanyar sauraron malamai, da kokarin dabbaka sunna a aikace. Duk da bai zamo mai ilimin zamani ba, yana da wayewar ganin diyarsa Nana ta samu ilimi mai zurfi don samun guzurin rayuwa da dogaro da kai. Dubi abin da yake cewa kan haka:

“… Batun makaranta dai, ina da burin ta ci gaba da karatu idan sakamakon jarabawarta ya fito. Ina son ko dai ta yi Babbar Difiloma ko kuma ta samu digirin jami’a. Batun aure kuwa, ai na gaya miki tun a baya, kofa a bude take. A duk lokacin da ta fito da manemi zan yi mata aure, ko da tana kan karatu ne. Idan da fahimta, ai neman iliminta ba zai hana ta aure ba.” (shafi na 24).

 

Zahra’u

Amarya, ’yar wan mahaifin Nana. Ta samu ilimi da tarbiyyar riko da Sunna. Duk da haka cikin rashin sani ta auri dan Shi’a. Sai dai kasancewar ta samu wayewa ta addini, ba ta yarda ta fada tarkon bin akidar angon nata Dangwaggo ba. Yayin da ya gayyato mata malaminsa don su taru su shawo kanta, cewa ta yi da su:

“… amma an yaudare ni ne har na samu kaina cikin wannan kuskuren. Iyayena da ni kaina ba mu san cewa Takiyya kuka nuna mana ba, amma na tabbata da mun san ku ’ya Shi’a ne tun da fari, babu mai yarda da kulla auren nan. Amma na gode Allah da ya fahimtar da ni tun yanzu da tafiyar ba ta yi nisa ba, da ka gama surutunka na wofi zan tafi gidanmu.” (shafi na 30).