Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa.
’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis ne suka samu kira daga Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Jigawa game da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawar zuwa Babban Asibitin Dutse, domin gudanar da bincike.