Gudanar da ma’aikata aiki ne da aka tsara ta yadda ma’aikata za ta ci moriyar ma’aikaci yadda ya kamata domin cimma manufofinta.
Gudanar da ma’aikata yadda ya dace na taimaka wa kasuwanci ya zarce sa’a, kuma yana bukatar amfani dabaru nagari domin ganin ma’aikata ta cimma muradunta.
Ayyukan sashen sun kunshi amfani da kwarewar ma’aikaci da fahimtar da basirarsa da kuma cin moriyar kwazonsa.
Sa’annan akwai kawo kyawawan sauye-sauye gudanar da huldar kasuwanci ko kuma tabbatar da ganin tsare-tsaren kamfani sun yi daidai da dokokin hukuma.
Fahimtar yadda zamani ke tafiya da neman ci gaba a bangaren gudanarwa ne ya sa Jami’ar Gudanar da Ma’aikata ta Sterling Bank Plc. ta fi mayar da hankali kan walwalar jama’a domin samun nasarar bankin.
“A bankin Sterling kokarinmu shi ne samar da jagorori daga cikin gida da kuma hulda da al’umma don cimma muradinmu na zama zabin jama’a.
“Hanyar da muke be domin cimma hakan it ace samar da yanayin aiki managarci.
“Shi ya sa muka fi ba da muhimmanci ga ma’akatanmu, su kuma suke ba kwastomomi da sauran al’umma muhimmanci.
“Mun yi ammanar cewa inda da hadin kai komai mai sauki ne, shi ya sa ba ma kasala wajen taimaka wa mabukata ko hada kai domin kirkiro da sabbin tsare-tsare”, inji ta.
She says the bank has built the concept of a home into the workplace by providing a space that is physically and mentally safe for employees. “Although the bank’s team is diverse, employees are happy to work and collaborate. The culture enables everyone and there are institutionalised systems that ensure our employees are protected and everyone is heard, seen, and safe,” she adds.
Ta ce bankin ya bullo da tsari da ma’aikaci zai sake a wurin aikinsa tamkar a gidansa.
“Duk da cewa ayyukan ma’aikatanmu sun bambanta, amma suna jin dadin yin aikinsu da kuma hada kai wanda hakan ke ba kowa kwarin gwiwar yin aikinsa da tabbacin samun kulawa da aminci”.
A yunkurin sauya abin da aka san aikin banki da shi nan da gajiya da damuwa, Sterlin Bank ya yi tsari da ma’aikaci zai kasance cikin koshin lafiya da kuma samun taimako.
Mun kuma tsara yadda ma’aikaci zai iya gudanar da aiki daga nesa ko kuma ya zabar wa kansa lokacin da zai yi aiki.
Hakan na ba ma’aikaci damar sada zumunci ko zama tare da makusantansa musamman a wuraren da ke fama da cunkoson ababen hawa.
“Duk dan hutun da aka samu zai taimaka”, inji ta. Sa’annnan bankin na da tsarin taimaka wa ma’aikatansa mata a kokarinsa an rage mace-macen mata masu ciki.
“Abu na gaba shi ne amfani da sakamakon binciken yanayin sakin fuska wajen gano yanayin da ma’aikatanmu ke ciki”, inji Dalley.
Bankin ya kuma tsarin yadda kowane ma’aikaci zai samu nutsuwar kai korafin abin da ya gani ba daidai ba a wurin aiki ta yadda kananan ma’ikata za su iya kai kara ko bayyana damuwarsu ga manyan manajoji da Manyan Daraktocin Gudanarwar”.
Ta ce Sterling Bank ya yi amannar cewa babu abun da ke dakile daukakar mutum face yanayin tunaninsa.
Shi ya sa ya ba wa kowa damar neman cigaba da daukaka.
Hakan ya ba wa ma’aikata damar karo ilimi da kuma samu karin matsayi ga ma’aikata.
Sauran sun hada da tukwici da Sterling bank ke ba ma’aikata nuna hazaka.
“Tsarin albashinmu na daga cikin mafiya kyau a bankuna kuma ya yi tasiri a lambar karramawa ta Jobberman da muka samu a matsayin daya daga cikin kamfanoni mafiya dacewa a yi hulda da su a Najeriya. Jobberman fitaccen dandalin na bayar da shawarwari da kwarin gwiwa a Najeriya.
Sterling Bank ya saukaka tsarin biyan albashi ta yadda ma’aikata na iya zabar yadda suke so a rika biyan su.
Ma’aikaci na iya zabar a biya shi wani bangare na albashinsa ko ma albashin kacokan kafin lokaci domin ya samu damar yin hidindimunsa.
“Bayan kashe kudade a hidindimun karshen shekara ma’aikaci ba shi fargabar biyan kudin makaranta ko na haya kuma za a ba shi kudaden ne gaba daya da zarar lokacin biya ya yi.
“Tsarin na Flex Pay tabbaci ne ga biyan bukatun ma’aikaci na kudade daban-daban”, inji jam’iar.
Ta ce, “Sanin muhimmanci ma’aikatanmu ya sa muka yi karin albashi da kashi 12 a 2019, domin kyautawa.
Lokacin da aka fara shiga dokar kulle a Legas da Abuja mun biya su albashi kwana biyar kafin lokaci albashi domin rage wa iyalansu tasirin kullen”.
Wani tsari da bankin ya yi shi ne ba da hannun jarinsa ga ma’aikata ta yadda kowane ma’aikaci ke mallakar hannun jarinsa a matsayin bangare na albashinsa, ba tare da la’akari da matsayin ko dadewarsa a kamfanin ba.
Akwai kuma tsarin tukwici da ya mayar da hankali wajen ganin ma’aikaci na samun albashi da alawus da kuma karin girma yadda ya dace gwargwadon kwarewarsa da hazakarsa.
An kuma yi tsarin tallaffin karatu da bankin ke daukar nauiyin ma’aikatansa su karo ilimi a matakin digiri na biyu ko na uku a Najeriya ko kasashen waje.
Akalla ma’aikata 250 sun ci gajiyar tsarin daga lokacin da aka fara shi a 2019 zuwa yanzu.
An kuma bullo da tsarin shugabanci na Sterling Bank Series domin musayar dabaru da tunani tsakanin matsakaita da manyan jami’an gudanarwa.
Zauren na ba wa shugabanni damar musayar ra’ayoyi da kulla dangantaka a fadin Afirka.
Sannan akwai tsari na musamman ga sabbin ma’aikata kan yadda za su samu fahimta da nutsuwar yin aiki a Sterling Bank.
“Muna tafiya daidai da bukatun aiki na zamani domin dacewa da bukatun kwararrun matasa a fagage daban-daban.
“Daga ciki akwai tsarin da kanana za su rika koyar da manya saboda muna da yakinin cewa karsashi da ilimin masu tasowa zai taimaka wa manya su koyi wani sabon abu da zai taimaka wajen cimma abun da bankin ya sa gaba.
“Mu a Sterling Bank baya ga samar da kyakkyawan yanayin aiki da bayar da damar samun cigaba, muna kuma bayar da damar nuna basira da kirkire-kirkiye.
“Domin tabbatar da daidaito tsakanin jinsi, muna daukar daukar dalibai mafiya hazaka domin tabbatar da cancanta da daidaito ta yadda yanzu kashi 53 na ma’akatanmu ne maza mata kuma kashi 47 tare da daidaito a albashin a kowane mataki.
Ta ca bankin ya gamsu cewa sauyi na da muhimmanci wurin kawo ci gaba da nagarta, shi ya sa ya riki wannan turba da ya kai shi ga zama kamfani mafi karsashi a 2018.
Sauran al’adun gudanarwa na Sterling Bank da takwarorinsa ke mamaki sun hada da tsarin tukwici ga hazikai a daidaikun ma’aikata ko cikin tawaga domin kara musu kwarin gwiwa.
Akwai kuma al’adar kiran juna da sunan yanka a kowane mataki wanda ke bayar da damar sakin jiki da junansu baya ga tarukan tattaunawa da Manajin Darekta bankin Abubakar Suleiman ke yi da kai tsaye da dukkanin ma’aikata a lokaci guda domin su saki jiki su fadi abin da ke damun su ba tare da fargaba ba.
Mun kuma yi tsarin sarrafa bayanai mai suna HCHub da ke taimaka wa samar da daidaito tsakanin amfani da fasahar zamani tare da bayar da muhimmanci ga dan Adam a kokarinta da rungumar fasahar zamani ka’in da na’in.
Wannan ya yi daidai da tsarin Taurarin Sterling Bankin da muka bullo da shi domin samar wa ma’aikata kudade da kuma tallafa wa kasuwancinsu.
Sterling Bank na burin samar wa ma’aikata wadatattun kayan aiki domin samun sakakmakon mai dorewa.
Shi ya sa yake ta sabunta shirinsa na kula da mutane domin tabbatar shugabanci managarci ta hanyar tsarin bin juna a wurin matsayin aiki.
Mayar da hankali da bankin ya yi wajen daukar koyon sabbin abubuwa ya taimaka wajen samun nasararsa a matsayin wajen aiki ta hanyar samar da horo da kwarewar da ta dace domin ba wa ma’aikta damar samun ci gaba.
Tsarin sa na koyarwa da karo basira da ya fara a 2019 ya horas da ma’aikata 2,000 baya ga shirin koyarwar kwararru na i-Learn da ya horas da mutum 200 cikin wata biyu da kafa shi, kuma zuwa yanzu ya horas da mutum 1,000.
Tabbas wadannan abubuwan da aka lissafo sun isa zama shaida cewa Sterling Bank ya cancanci kyaututtukan da ya samu a matsayin wuri na uku mafi dadin aiki a Najeriya/Afirka; kamfanin da ya fi bayar da tallafin da ya dace da zamani; daya daga cikin manyan kamfanoni 100 a Najeriya; jagora a harkar shugabanci da gudanar da ma’aikata da huldar kudi da dai sauransu.