✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wulaƙancin da ake mana a Kudu ya yi yawa —Hausawan Legas

Samarin Yarabawa daga wasu unguwanni sun mayar da yankin Hausawa filin ƙwallon ƙafa, inda suke tilasta musu rufe shaguna har sai an gama buga ƙwallo

Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi.

Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna.

Sun bayar da misali da yadda samarin Yarabawa daga wasu unguwanni suka mayar da unguwar tasu filin ƙwallon ƙafa, inda suke tilasta musu rufe shaguna, har sai an gama buga ƙwalon kafin su ci gaba da sana’arsu.

A kan haka ne suka yi wani zama da Shugaban Karamar Hukumar Ikoyi Obalande (LCDA) Fu’ad Lawal Atanda da shugabannin siyasa ’yan Arewa a jihar, da nufin cire kitse daga wuta.

Taron ya kuma tattauna kan matsalar lalacewar tarbiyya da shaye-shaye da karuwanci da baɗala da wasu matasan yankin da sauran ɓata-gari ke yaɗawa.

Yadda ake mana cin kashi — Gulma

Jagoran taron kuma Shugaban Majalisar Shugabannin ’Yan Arewa na Ƙananan Hukumomim Jihar Legas, Alhaji Sa’adu Gulma, ya shaida wa Aminiya cewa, dalilin shirya taron shi ne ƙalubalen da ’yan Arewa ke fama da su cikin unguwar Obalende.

Alhaji Sa’adu Gulma, wanda ya ce ya fi shekara 40 a Obalende, ya ce “Yarabawan wasu unguwanni ke shigo mana, su tilasta wa ’yan kasuwarmu rufe rumfunan kasuwanci da sunan buga ƙwallon ƙafa. Ku ma ’yan jarida a yau kuna gani yadda matasan Yarabawan suka rufe mana layi, suna buga ƙwallo, sun tilasta wa ’yan kasuwarmu rufe kantinansu.

“Haka suke yi, wani lokaci sai su zo nan tun safe ba za za su tashi ba sai bayan sallar Azahar, babu Lahadi, babu Litinin duk lokacin da suka ga dama suke shigo mana, ba ka isa ka buɗe kantinka ba, saboda suna ƙwallo.

“Waɗannan abubuwan ne ke ci mana tuwo a ƙwarya da suka sa muka farka, muka kira wannan taro, domin mu sama wa kanmu mafita. Idan muka haɗa kai muka nema wa kanmu mafita, za su kiyaye mu, domin sai bango ya tsage ƙadangare zai shiga, ya sami mafaka.

“Ba za mu yarda amfaninmu ya zama kawai lokacin siyasa ba, ta yadda za a yi amfani da mu idan an ci moriyar ganga a jefar da kaurenta” in ji shi.

‘Ko a mafarki ban tava tunani ba’

Game da lalacewar tarbiyya a yankin, Alhaji Zakari Zaki, ya ce, ko a mafarki bai taɓa tunanin abin da ke faruwa a yankin ba.

Ya shaida wa Aminiya cewa, “Na kasance a wannan unguwar sama da shekara 43, kuma a wancan lokacin abin da ke faruwa a yanzu ko a marfarki ban taɓa zaton za mu sami kanmu cikin wannan hali ba, kuma kowa ya yi shiru.

“Abu na farko babu shugabanci, abin da ya sa na ce babu shugabanci, a baya muna da Shugaba Hamza Kolo, a nan zai fito shan iska za ka ga manyan shugabannin ƙasa irin su Abacha da Babangida da sauransusu, sun zo sun zauna tare da shi, suna hira.

“A wancan lokacin babu shiririta irin su harkar shaye-shaye ko karuwanci a nan, sai dai kyawawan al’adunmu na gargajiyar Arewa, amma a yanzu a wannan unguwar zai yi wuya ka bambamce matar aure da karuwa.

“Sannan abu na biyu mutanenmu da ke shigowa kasuwanci ya kamata su sani kowace jiha da irin tata doka da ƙa’idoji. Mutum ne zai zo ya kasa kayan kasuwancinsa a kan hanya, idan ka yi masa magana sai ya ce ‘ai ba kai ka kawo ni Legas ba’. Ka ga wannan matsala ce ta rashin shugabanci.”

Za mu ƙungiyar aiki da cikawa — Zaki

Ya ce, “bayan taron za mu kafa ƙungiyar haxaka ta tabbatar da tsaro da doka da oda a unguwar ta Obalende, kuma za mu kafa ta bisa doka, za mu tuntubi duk mahukunta da suka da ce” in ji shi.

Wazirin Obalende, Alhaji Sale Muhammed Waziri, wanda yana cikin mahalarta taron ya shaida cewa, tabbas mawuyacin halin da Hausawa da sauran ’yan Arewa ’yan Obalende suka sami kansu shi ne rashin shugabanci ko jagoranci na gari.

Ya ce, “Tun da asalin shugabanninmu na baya suka rasu, an rasa waxanda za su jagoranci al’amarin talakawa a Obalende.

“Idan babu shugabanci kyakkyawa, su ma talakawan ba za su zamo masu biyayya ba. Muna fatan kuma a aiwatar da abubuwan da aka faɗa a wajen wannan taro, domin galibi sai an taru an yi gangami an yi abu sai ka ga daga baya an rushe shi, ba a aiwatar da komi ba.

“Muddin za a aiwatar da abubuwan da aka cim ma muna fatan wannan unguwa ta Obalende za ta sami ci gaba, kuma sauran unguwannin Hausawa a Legas za su yi koyi da Obalende”, in ji shi.

‘Abin da ya jawo mana ƙasƙanci a Legas’

Alhaji Sa’adu Gulma ya ce rashin tsari ne ke janyo wa ’yan Arewa mazauna Legas ƙalubalen da suke fuskanta. Ya ce kaɗan daga cikin rashin tsarin sun haɗar da rashin amfani da tsarin katin shaida.

“Mutum ne zai baro gida Arewa, ya zo ci-rani Legas ba shi da wata takarda ko katin shaida da zai nuna daga inda ya fito ko kalar sana’ar da yake, da zarar ya shiga matsala an kai shi gidan yari shi ke nan, babu yadda za a gano ’yan uwansa.

“Idan an zo kame daman shi ba shi da katin shaida, ba za a gane ko na gari ba ne ko ɓata-gari ne, don ba shi da alamar da za a tantance shi. Wannan kaɗan ne daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta.

“Su ragowar ƙabilu kowace irin sana’a suke, komai ƙanƙantarta za su yi ƙungiya, za su sami katin shaida na mambobinsu, amma mu a ɓangarenmu na ’yan Arewa muna zaune ne kara zube, dole sai mun gyara kafin mu ga ci gaba.

“Za mu yi zama na musamman da sauran shugabannin ’yan Arewa na Obalende, domin samar da mafita ga matsalolin da ke addabar su”, in ji shi

Gwmanati za ta ɗauki mataki — Ciyaman

Da yake magana a kan koke-koken, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya bayyana cewa tarihi ba zai manta da irin gudummawar da iyaye da kakannin ’yan Arewa mazauna Obalande suka bayar ba, yana mai cewa, ya san lokacin da duk wani babba da suka haɗar da shugabannin ƙasa da ’yan majalisun a jamhuriya ta farko suke zuwa Obalande a yi masu ɗinki.

“Yawancin manyan mutanen nan tailolinsu a nan Obalande suke, nan suke zuwa su huta, bayan sun kammala sha’anin mulkin ƙasa, nan suke cin abinci irin na gargajiyarsu, a nan ake yi masu ɗinkuna irin na gargajiya, kuma wannan yanki ne mai zaman lafiya da ba a taɓa samun rikici ko na ƙabilanci ko kuma wani na daban ba.

“Don haka za mu yi duba ga duk matsalolin da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kuma maganar masu yin ƙwallo cikin unguwarku, tuni muka samar da filayen ƙwallo, wanda za su iya zuwa can su yi amfani da su, ba tare da sun shigo nan sun addabe ku ba,” a cewarsa.

Fu’ad Lawal ya ce, taron ba na siyasa ba ne, illa kawai a duba hanyoyin magance matsalolin da ke addabar ’yan Arewan, “amma ba zan mance da irin gudummawar da kuka ba ni ba a siyasance tsawon shekaru takwas da na yi ina jagorancin wannan ƙaramar hukuma,” In ji shi.