✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wizkid ya lashe kyautar mawakan Afrika ta AFRIMA

An dai gudanar da gasar ne a birnin Legas ranar Lahadi.

Fitaccen mawakin Kudancin Najeriya mai salon kidan Afrobeats, Ayo Balogun wanda aka fi sani da Wizkid,  ya lashe kyaututtuka a bikin bayar da kyautar mawaka ta AFRIMA 2021.

An dai gudanar da gasar ne a birnin Legas ranar Lahadi.

Mawakin dai ya lashe kyautar mawakin shekara, wakar shekara da kuma wakar hadin gwiwa ma fi shahara a bikin da aka gudanar a birnin Legas.

Shi ma wawakin Najeriya, Fireboy DML ya karbi kyautar masoya yayin da mawakiyar kasar Kenya, Nikita Kering, ta karbi kyautar gwarzuwa a salon wakar RnB.

Sai dai wanda ya fi kowa haskawa a bikin shi ne Iba One, mawakin kasar Mali wanda ya lashe kyautattuka biyar a tashi daya.