Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi bankwana da maniyyata 966 da za su je aikin Hajjin bana, inda ya buƙace su da su kiyaye dokoki da tsarin ƙasar Saudiyya.
Gwamnan, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, wanda ya gargaɗi maniyyatan da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci.
- Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma
- NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a?
Gwamnan ya bai wa kowane maniyyaci kyautar Riyal 200 a matsayin goron Sallah.
An kuma ja hankalin maniyyatan da ka da su karɓi kaya ko rigar wani, ko da ’yan jiharsu ne, don kauce wa matsala.
Malaman addini da suka halarci taron sun shawarci maniyyatan da su yi aikin Hajji da nufin samun lada, su nemi ƙarin haske idan ba su fahimci wani abu ba, sannan su yi addu’a don samun zaman lafiya a Najeriya.
Hakazalika, an tunatar da su, su kula da kayansu don kaucewa shiga matsala.
Sakataren hukumar Alhazai na jihar, Alhaji Sa’adu Hassan, ya bayyana cewa aikin Hajji ibada ce, ba yawon shaƙatawa ba, don haka ya buƙace su, da su mayar da hankali wajen gudanar da ibadarsu.