Fitaccen mawakin Kudancin Najeriya mai salon kidan Afrobeats, Ayo Balogun wanda aka fi sani da Wizkid, ya lashe kyaututtuka a bikin bayar da kyautar mawaka ta AFRIMA 2021.
An dai gudanar da gasar ne a birnin Legas ranar Lahadi.
- Mutum biyar da ka iya maye gurbin Solskjaer a Manchester United
- Mutane da dama sun mutu bayan tashin gobara a tashar jiragen ruwa a Fatakwal
Mawakin dai ya lashe kyautar mawakin shekara, wakar shekara da kuma wakar hadin gwiwa ma fi shahara a bikin da aka gudanar a birnin Legas.
Shi ma wawakin Najeriya, Fireboy DML ya karbi kyautar masoya yayin da mawakiyar kasar Kenya, Nikita Kering, ta karbi kyautar gwarzuwa a salon wakar RnB.
Sai dai wanda ya fi kowa haskawa a bikin shi ne Iba One, mawakin kasar Mali wanda ya lashe kyautattuka biyar a tashi daya.