Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro a sakamakon tabarbarewar sha’anin tsaro a sassan babban birnin.
Zaman nasa da shugabannin hukumomin tsaro da shugabannin kananan hukumomi da sarakunan gargajiya na gudana a halin yanzu.
Gabanin fara zaman, ministan ya bukaci hukumomin tsaro da su sabunta dabarun aikinsu domin dakile duk wata barazanar tsaro da kuma tabbatar da aminci a fadin Abuja.
Hakazalika ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomi da su yi tsayuwar daka wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.
Ana zaman gaggawan ne kwanaki kadan bayan kisan gilla da ’yan bindiga suka yi wa wata dalibar aji biyar a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Nabeeha Al-Kadariya tare da wasu musu mutum uku.
Sauran wadanda aka kashe din sun hada da wata dalibar sakandare mai shekaru 13, Folorunsho Ariyo, wadda aka sace tare da mahaifiyarta da yan uwanta uku.
An kashe Nabeeha ne bayan an sace ta tare da mahaifinta da ’yan uwanta mata biyar, daga bisani aka sako mahaifin don ya kawo kudin fansarsu Naira miliyan 60 cikin kwana uku.
Rashin samun kudin ya sa aka kashe ta aka kara kudin zuwa milian 100.
Ita kuwa Folorunsho tana cikin mutane 10 da aka yi garkuwa da su, inda aka kashe su su uku saboda rashin kawo kudin fansa, sannan aka kara yawan kudin zuwa miliyan 100 a kan kowannensu da ke raye.
Matsalar tsaro ta kara kamari a Abuja a baya-bayan nan, inda ’yan bindiga ke kari hari a cikin birane suna sace jama’a domin karbar kudin fansa.
Wannan wani sabon salo ne, kasancewa kafin wannan lokaci a kauyuka ake samun matsalar.