Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya haramta tallace-tallace da kuma saye da sayarwa a gefen titunan birnin Abuja.
Wike ya bayyana cewa ya yi amanna cewa masu tallace-tallace da masu kasa kaya a gefen tituna na ba da gudunmawa wajen taɓarɓarewar tsaro da kuma aikata miyagun laifuka a Abuja.
- NAJERIYA A YAU: Ta ya Ministocin Tinubu za su cika alƙawuran da suka yi?
- Gwamnan Kano zai biya wa daliban BUK 7,000 kudin makaranta
Don haka ya ce, “Dole mu kawar da masu tallace-tallace daga titunan,” saboda yadda suke kawo ƙazanta da kuma taimakawa wajen taɓarɓarewar tsaro.
Da yake jawabi ga manyan jami’an kula da kuma bunƙasa birnin, Wike ya kuma umarce su da su kawo ƙarshen yadda mutane ke ajiye motoci barkatai a birnin nan ba da jimawa ba.
Sannan ya hore su da su yi abin da ya dace wajen dawo da martabar Abuja a matsayinta babban birnin tarayya kuma fadar gwamnati.
“Abu mafi muhimmanci shi ne, dole ne mu tabbatar da cewa, Abuja ta dawo da martabarta kuma yadda aka tsara ta tun asali.
“Na kuma kewaya sassan Abuja, kuma na gano cewa, akwai duhun rashin wutar lantarki a wurare masu yawa.
“Saboda haka, abin da za mu yi shi ne, tabbatar da samuwar wutar lantarki nan ba da jimawa ba,” in ji Wike.