✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wike ya dawo Najeriya bayan ganawa da ’yan takarar Shugaban Kasa a Landan

Wike da wasu gwamnonin PDP uku sun yi ziyarar kwana biyar a Landan.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya koma Fatakwal, babban birnin jihar bayan ziyarar kwana biyar da ya kai birnin Landan na kasar Birtaniya.

A cewar mataimaki na musamman ga gwamnan a kan kafafen sada zumunta, Marshall Obuzor, Wike ya isa filin jirgin saman Fatakwal da karfe 3.20 na Yammacin ranar Juma’a.

Gwamnan ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu da Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom.

Jim kadan bayan isowarsu, Gwamna Ortom ya ce Wike da ayarinsa sun gana da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.

Ya ce, taron da Wike ya yi da ’yan takarar Shugaban Kasa uku ya yi matukar amfani kuma yana da manufar ciyar da Najeriya gaba.