✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wike ya ba ’yan gudun hijirar Kaduna tallafin N200m

Ya bayar da tallafi ne a ci gaba da rangadinsa na neman takara a PDP

Gwamnan Ribas, Nyesam Wike ya ba da tallafin Naira miliyan 200 ga sansanonin ’yan gudun hijira da ke Jihar Kaduna domin kula da mutanen cikinsu.

Gwamna ya ba da tallafin ne yayin ziyararsa ga sakatariyar jam’iyyar PDP ta Jihar ranar Litinin, a rangadinsa na neman Shugabancin Najeriya a 2023.

“Ba za mu daga kafa a kokarinmu na samun nasarar zaben ba, don haka muna bukatar jajirtattun ’yan takara, kuma hakan ba zai samu ba har sai kun ba mu amincewa,” inji Wike.

Ya ce babban abin da ya kamata kowacce gwamnati da ta san me take yi ta yi da zarar ta dare karagar mulki shi ne kawo karshen kalubalen tsaro da ya addabi Najeriya.

Don haka ya ce abin da zai mayar da hankali a watanni shidansa na farkon mulkinsa da zarar ya ci zabe shi ne dawo da zaman lafiya a Jihohi.

Wike ya ce muddin ya gaza a kan haka, to mulkinsa zai zama mara amfani, saboda ya ce duk Shugaban da ba zai iya haka ba, to shugabancinsa bai da amfani.

Kazalika ya ce gwamnatocin kasar nan na bata lokaci da dukiyar al’umma a siyan makamai a maimakon su mayar da hankali kan tattara bayanan sirri.

A nasa bangaren, tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmad Makarfi, ya yaba wa Gwamna Wike bisa jajircewarsa.

Shi ma Shugaban PDP na Kaduna Mr Felix Hyet ya ce jam’iyyar a shirye take ta tsaida ’yan takarar da za su yi daidai da ra’ayin al’umma kuma wakilan talakawan kasa.

%d bloggers like this: