Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da takwaransa na Binuwai, Samuel Ortom sun kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sunayen gwamnonin da yake zargi da satar kudaden kananan hukumomi.
A ranar Alhamis aka ji Shugaba Buhari ya ce wasu gwamnoni na wawushe kudaden da aka ware don amfanin kananan hukumomi.
Washegari kuma, gwamnonin Ribas da Binuwai sun kalubalance shi ya fito ya bayyana gwamnonin da yake zargi da wannan aika-aikar.
Wike ya ce tun da ya zama gwamna a 2015, bai taba daukar kudin da aka ware wa kananan hukumomin jiharsa ba.
Ya ce, lallai ne Buhari ya fito ya bayyana sunaye ko kuma kalamansa su zama na bata suna.