Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Gebreyesus, ya gana da Ministan Lafiyar Taliban da ke kasar Faransa dangane da tabarbarewar ayyukan jinkai a kasar Afghanistan.
Gebreyesus, ya ce sun tattauna da Qalender Ebad wanda ke cikin tawagar Taliban da ta kai ziyara birnin Geneva na kasar Switzerland domin tattaunawa da hukumomin duniya.
- Ta’aziyyar Hanifa da Ahmad Bamba ta kai Aisha Buhari Kano
- AFCON 2021: An yi wa tawagar Senegal ruwan kudi da filaye
Shugaban WHO, ya ce duk da dan cigaban da aka samu a Afghansitan, har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da ayyukan jinkai wanda ke jefa rayuwar jama’a cikin mawuyacin hali.
Kazalika, ya ce sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi bunkasa harkokin lafiyar jama’a da ayyukan agajin gagagwa da kuma batun horar da ma’aikatan lafiya a Afghanistan.
Ya ce babbar bukatar Afghansitan a yanzu ita ce samun kayan gwajin cutar COVID-19, musaman nau’in omicron ganin yadda adadin masu kamuwa da cutar ke yawaita a kasar.
Gwamnatin Switzerland ta gayyaci wakilan gwamnatin Taliban ne domin tattaunawa da su a kan ayyukan jinkai da kuma bada ilimi.
A baya-bayan nan gwamnatin Taliban ta nemi dauki daga kasashen duniya su tallafa mata duba da yadda tattalin arzikin kasar ke kara durkushewa tun bayan da ta karbi mulki.