✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘White Money’ ya zama gwarzon shirin BBNaija na 2021

White Money ya sami nasarar ne bayan doke abokan fafatawarsa a cikin shirin.

Hazel Oyeye Onuo, wanda aka fi sani da ‘White Money’ zai tafi gida da kyaututtukan da darajarsu ta kai Naira miliyan 90 bayan ya zama zakaran shirin Big Brother Naija na 2021.

White Money, wanda Dan asalin Jihar Enugu ne, ya lashe gasar ne bayan ya doke abokan fafatawarsa a cikin shirin.

Liquorose dai ita ce ta zo biyu, yayin da Pere ya rabauta da mataki na uku.

Hakan dai na nufin White Money zai tafi da tsabar kudi har Naira miliyan 30 da kuma wani gida mai daki biyu da kamfanin Renovation Plus ya ba shi.

Kazalika, ya kuma sami kyautar mota kirar Innoson IVM G40 da tafiya hutu zuwa Dubai don shakatawa da kamfanin TravelBeta zai dauki nauyinsa shi da wani.

Zai kuma karbi kyaututtukan kudi daga Abeg Wallet da Patricia, tafiya hutun karshen mako zuwa kasar Seychelles da kamfanin Diageo zai dauki nauyinsa, da kyautar katan-katan na kayan kamfanin Dano, sannan ya sami kyautar kayan kamfanin Pepsi da zai yi amfani da su na tsawon shekara guda.

Sauran kyaututtukan da White Money ya samu sun hada da kayan Munch It, da na kamfanin Tecno, ciki har da waya kirar Phantom X da kuma omon kamfanin WAW da kuma sabulun Hawaii.