Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce an samu saukar yawan hauhawan farashin kayayyaki a watan Janairun 2022 a Najeriya, idan aka kwatanta da watan Disambar 2021.
A cewarta, an samu raguwar da kaso 0.03 cikin 100, ragi a kan kaso 15.63 din da yake a watan Disamban na bara.
- Buhari ya mika wa Majalisa kasafin tiriliyan 2.557 don biyan tallafin man fetur
- HOTUNA: Yadda karancin mai ya kawo cikas ga harkar sufuri a Abuja
Masana dai na alakanta karuwar a wancan lokacin da yawan kashe-kashen kudaden da ake yi a watan Disamba, wanda ya kan jawo hauhawar farashin kayayyakin.
Babban Mai Kididdiga na Kasa kuma Shugaban hukumar ta NBS, Dokta Simon Harry, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Talata.
Ya ce an samu karin ne a watan Disambar saboda tashin farashin kayayyaki irinsu dankalin Turawa da doya da rogo da lemukan kwalba da kuma kayan itatuwa.
Dokta Harry ya ce farashin kayan da ba na abinci ba ya karu da kaso 1.62 a watan Janairun 2022, wanda ya ragu da kaso 0.57 daga kaso 2.19 da aka samu a watan Disamban na bara.
“Kayan da aka fi samun hauhawar farashin a kansu fiye da kowanne sun hada da wutar lantarki, man fetur da barasa da sigari da man shafawa da na girki da kayan shara da kuma bangaren suttura da takalma.
“Kazalika, an samu kari a bagaren kayan sufuri da kuma bangaren magunguna,” inji shugaban na NBS.